Kano: Ahmed Musa Ya Dauki Zafi Kan Cece Kuce da Ake Yi Bayan Kin Gaisawa da Abba Kabir

Kano: Ahmed Musa Ya Dauki Zafi Kan Cece Kuce da Ake Yi Bayan Kin Gaisawa da Abba Kabir

  • Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ya nuna damuwa kan yadda ake cece-kuce bayan kin gaisawa da Gwamna Abba Kabir
  • Musa ya ce abin takaici ne yadda bayan faruwar abin da wata guda ake ta cece-kuce duk da matsalolin da kasar ke ciki
  • Ya bayyana cewa wasu da yawa ba su sani ba abin da ya yi ba rashin tarbiya ba ne, hasalima ya na daga cikin al’adun Hausawa a Arewa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Fitaccen dan wasan Super Eagles, Ahmed Musa ya yi martani kan cece-kuce game da kin gaisawa da Gwamna Abba Kabir.

Musa ya kare kansa inda ya ce ya yi hakan ne saboda girmamawa ga gwamnan inda ya bukaci mutane su mayar da hankali ga abubuwan ci gaban kasa.

Kara karanta wannan

Rikicin El-Rufai da Uba Sani: Shehu Sani ya fadi gaskiyar lamari kan bashin Kaduna

Ahmed Musa ya fusata kan cece-kuce da ake yi game da kin ba da Abba Kabir hannu
Ahmed Musa ya yi karin haske kan kin ba Abba Kabir hannu. Hoto: @ahmedmusa718.
Asali: Instagram

Martanin Ahmed Musa kan lamarin

Wannan martani ya biyo bayan wani faifan bidiyo da ake yadawa inda ya Musa gaisa da mataimakin gwamnan amma ya ki gaisawa da Abba Kabir duk da durkusawa da ya yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A martaninsa, Musa ya ce abin takaici ne yadda ake yada bidiyon bayan abin ya faru fiye da wata daya.

“Na ga ana ta yada wani bidiyo da aka dauka fiye da wata guda, lamarin ya jawo cece-kuce a kafafen sadarwa, abin takaici ne mutane ba su fahimci mutuntawa ta al’ada ba.”

- Ahmed Musa

Ya bayyana amfanin abin da ya aikata inda ya ce wannan na daga cikin al’adun mutuntawa na al’ummar Hausawa a Arewacin Najeriya.

“A al’adunmu na Arewacin Najeriya, gaisuwa da durkusawa na daga cikin mutuntawa, wannan na daga cikin dalilan da ya sa na gaishe da mataimakin gwamnan.”

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya fadi wahayin da ya samu kan wa'adin da shugaban zai yi a mulki

“Lokacin da na zo gaishe da Gwamna, na yi tunanin durkusawa ba tare da mika masa hannu ba wanda hakan ke nuna tsantsar mutuntawa.”

- Ahmed Musa

Ya shawarci maida hankali kan matsalolin kasa

Musa ya koka kan yadda lamarin ya yi ta yawo har da manyan jaridun kasar inda ya ce ya kamata a maida hankali kan matsalolin kasar.

Ya kara da cewa babban abin takaici ma shi ne yadda ake kokwanton tarbiyarshi musamman ga wadansu da ba su san asalinsa ba.

Musa ya yi magana kan makomarsa

Kun ji cewa dan wasan Super Eagles, Ahmed Musa ya ce a kullum shirye ya ke idan ana bukatar taimakonsa a kungiyar.

Musa ya bayyana haka ne yayin da ake ta cece-kuce kan cewa bai buga ko da wasa daya ba a gasar AFCON.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.