'Yan Bindiga Sun Kashe Babban Ɗan Kasuwa a Arewa, Sun Ɗauke Matarsa da Maƙwabcinsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Babban Ɗan Kasuwa a Arewa, Sun Ɗauke Matarsa da Maƙwabcinsa

  • Yan bindiga sun shiga har cikin gidan wani ɗan kasuwa, sun kashe shi tare da sace matarsa da maƙwabcinsa a jihar Zamfara
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Shehu Muhammad Dalijan, ya tabbatar da faruwar lamarin a Gusau, babban birnin jihar
  • Amma kwamishinan ya musanta harin da ake cewa wasu ƴan bindiga sun shiga masallaci ana sallar Tahajjud a Gusau

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani ɗan kasuwa tare da sace matarsa ​​da makwabcinsa a unguwar Buluku da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Buluku dai wata unguwa ce da ke bayan gidan talabijin na Najeriya (NTA) a cikin babban birnin jihar ta Arewa maso Yamma, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun yi kazamin artabu da ƴan bindiga, mutane da yawa sun mutu

Yan sanda.
CP ya ce ba a kai hari masallaci ba, wani ɗan kasuwa aka kashe a Gusau Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

Wani mazauni, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ‘yan bindigar sun shiga gidan ɗan kasuwar kuma dillalin abubuwan sha, domin su sace wasu mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"‘Yan bindigar sun yi yunkurin sace mutumin amma da ya yi turjiya sai suka kashe shi suka tafi da matarsa ​​da makwabcinsa,” in ji majiyar.

Ƴan sanda sun tabbatar da lamarin

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, CP Shehu Muhammad Dalijan, ya tabbatar da kashe dan kasuwar tare da yin garkuwa da mutane biyu a harin.

Tun farko, jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda wasu gungun ƴan bindiga suka farmaki masallaci, inda suka yi awon da gaba da masallata ana tsaka da sallar dare Tahajjud.

Tahajjud wata sallar nafila ce da musulmai ke yi a tsakiyar kowane dare a goman ƙarshe na watan azumin Ramadana.

Kara karanta wannan

Daga karshe Wike ya bayyana inda aka kwana kan rikicinsa da Gwamna Fubara

CP ya musanta kai hari masallaci

Amma dai kwamishinan ƴan sandan jihar ya musanta kai hari masallaci a Gusau, jihar Zamfara.

"Babu wani hari da aka kai masallaci tare da sace masu sallah, abin da ya faru shi ne ƴan bindiga sun shiga gidan wani ɗan kasuwa, suka yi kokarin tafiya da shi.
"Yayin da ɗan kasuwar ya masu turjiya shi ne suka kashe shi, sannan suka tafi da matarsa da makocinsa."

- CP Shehu Muhammad Dalijan.

Wani mazaunin Gusau da ya nemi a ɓoye sunnasa saboda dalili na tsaro ya shaidawa Legit Hausa cewa ya samu tabbacin ƴan bindiga sun kai hari masallaci.

A cewarsa, ya tsammanin ƴan sanda ba su samu rahoton harin bane amma an kai harin tare da sace masallata ciki har da limamin sallar Tahajjud.

"Akwai abokina ɗan unguwar kuma har ɗakina ya zo yana bani labari, kuma limamin da aka ce an sace ba a ganshi a wurin sallar subahi a ranar ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai harin rashin imani ana azumi, sun yi garkuwa da kananan yara 30 a Arewa

"Ban san wane bayani ƴan sanda suka yi amfani da shi ba amma ni dai na samu labarin kai harin, Allah ya kawo mana karshen lamarin nan," in ji shi.

An sace kanana yara 30 a Katsina

A wani rahoton kuma Ƴan bindiga sun sake jefa mutane cikin tashin hankali yayin da suka sace kananan yara 30 a wani kauyen ƙaramar hukumar Batsari a Katsina.

Rahoto ya nuna cewa tun farko yaran sun fita gefen gari domin ɗibo itacen girki amma ƴan bindiga suka tattara suka tafi da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262