Sauki Ya Zo Yayin da Dangote Ya Fara Siyar da Mai, Ya Gindaya Ka’idoji Ga ’Yan Kasuwa
- Jama'a sun fara murna yayin da aka fara siyar da mai a matatar fitaccen dan kasuwa a Afirka, Aliko Dangote
- Shugaban dillalan mai a Najeriya, Abubakar Maigandi shi ya tabbatar da haka a yau Talata 2 ga watan Afrilu
- Kamfanin ya sanar da cewa zai rika siyar da man ne ga 'yan kasuwa mafi karanci a lita miliyan daya ga kowane dan kasuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Matatar man Aliko Dangote za ta fara siyar da mai a yau Talata 2 ga watan Afrilu ga 'yan kasuwa.
Matatar ta shirya fitar da ganguna 650,000 a kowace rana inda ta gindaya sharuda ga 'yan kasuwar mai a Najeriya.
Kaidar matatar Dangote ga 'yan kasuwa
Kamfanin zai rika siyar da litar mai miliyan daya ne mafi karanci ga kowane dan kasuwa, a cewar rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban dillalan mai a Najeriya, Alhaji Abubakar Maigandi ya fitar a yau Talata 2 ga watan Afrilu.
Ya ce mafi karancin abin da dan kasuwa zai iya siya shi ne lita miliyan daya kamar yadda kamfanin ya sanar.
Yaushe za a fara saida man Dangote?
"Mafi karancin yawan litar mai da dan kasuwa zai siya shi ne miliyan daya, a yanzu haka na kira wani ya tabbatar cewa za su fara siyarwa."
- Abubakar Maigandi
Ya ce a akwai bayanai gamsassu cewa matatar za ta fara siyar da man a yau Talata 2 ga watan Maris, cewar Inside Business.
Sai dai jami'in yada labaran kamfanin Dangote, Anthony Chiejina bai yi martani kan sakon da aka tura masa ba.
Kamfanonin da za su yi dallancin man Dangote
Kun ji cewa Manyan 'yan kasuwa bakwai a Najeriya sun yi rajista da matatar mai ta Dangote domin dillancin man fetur da matatar za ta rinka fitarwa.
Dillalan wadanda ke karkashin kungiyar manyan dillalan man fetur ta Najeriya sun bayyana cewa da zaran sun kammala sa hannu kan yarjejeniyar za su fara dillancin man.
Wannan na zuwa ne bayan kamfanin ya shirya fara siyar da man a Najeriya musamman ga 'yan kasuwa.
Asali: Legit.ng