Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda Ya Halaka Kansa Ta Hanyar Rataya
- Rahotannin da muke samun yanzu na nuni da cewa wani mataimakin kwamishinan'yan sanda, Gbolahan Oyedemi ya halaka kansa
- An rahoto Oyedemi wanda tsohon dogarin tsohon gwamnan Oyo ne, ya halaka kansa ta hanyar rataya a gidansa da ke Ogbomoso
- Wata majiya daga iyalan mamacin, ya bayyana cewa mataimakin kwamishinan ya ziyarci Ogbomoso ne domin bikin Easter
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Oyo - Wani mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Gbolahan Oyedemi ya halaka kansa a cikin gidansa da ke garin Ogbomoso, jihar Oyo.
Mataimakin kwamishinan ya je hutun Easter
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Oyedemi na aiki ne a sashen rundunar binciken laifuffukan ta'addanci na ofishin 'yan sandan Alagbon, jihar Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Oyedemi ya kuma taba zama dogarin tsohon gwamnan jihar Oyo, marigayi Adebayo Alao-Akala, a watanni 11 da yayi kan mulki.
Wata majiya daga iyalan mamacin, ta shaidawa jaridar The Nation cewa Oyedemi na ziyartar gidan nasa ne a lokutan bikin Easter.
Oyedemi ya mutu ta hanyar rataya
Majiyar ta bayyana cewa a wannan shekarar, mataimakin kwamishinan ya sahalewar masu taimaka masa da su tafi gidajensu su yi hutu tare da iyalansu.
A cewar majiyar:
"Tabbas, ya halaka kansa ne. Mun samu gawarsa rataye a cikin gidansa a jiya (Litinin). Shi kadai ne dama a gidan, ya kan zo a lokutan Easter."
A cewar rahoton jaridar The Sun, duk wani yunkuri na jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Adewale Osifeso ya ci tura.
Sufetan 'yan sanda ya halaka kansa
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito yadda wani sufetan 'yan sanda, Nelson Abuante ya bindige kansa bayan da ya yi kuskuren harbin abokin aikinsa har lahira a jihar Ribas.
Lamarin ya faru ne a lokacin da Sufeta Abuante da Sufeta Monday Gbramma suka je kamo wani mai laifi, sai dai mai laifin ya nuna gardama inda Abuante ya yi yunkurin tsoratarshi da bindigar.
Cikin rashin sa'a, bindigar ta tashi tare da harbin Sufeta Gbramma, wanda ya mutu a hanyar kai shi asibiti, inda ganin hakan ya sa shi ma Sufeta Abuante ya bindige kansa har lahira.
Asali: Legit.ng