Jami’in Dansanda ya dirka ma kansa harsashi bayan ya bindige matarsa har lahira

Jami’in Dansanda ya dirka ma kansa harsashi bayan ya bindige matarsa har lahira

Rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Ondo ta bayyana cewa tana gudanar da binciken kwakaf bisa wani mummunan lamari daya faru a jahar inda wani Dansanda ya halaka kan sa bayan ya kashe matarsa.

Daily Trust ta ruwaito dansandan mai suna Sajan Saliu Tolulope ya dirka ma matarsa bindiga ne, sa’annan ya bindige kansa har lahira a makon da ta gabata a unguwar Akungba-Akoko na karamar hukumar Akoko ta Yamma a jahar Ondo.

KU KARANTA: Sojoji 6 sun mutu a harin kwantan bauna da Boko Haram ta kai a Borno

Lamarin ya faru ne a gaban yaran mamatan biyu, inda babban yake dan shekara 2, karamin kuma bai wuce watanni uku da haihuwa ba. Makwabtan su sun tabbatar da cewa sun ji yo muryar ma’auratan suna cacar baki, daga nan sai kawai suka ji karar harbin bindiga, koda suka garzaya gidan sai dai gawarsu kawai suka tarar.

Wata majiya ta shaida cewa matar Dansanda Saliu ta kai masa ziyara ne tare da yaranta biyu sakamakon bai dade da aka tura shi Akoko ba, sai dai a yayin ziyarar ne cacar baki ta kaure tsakaninsu game da zargin cin amana.

Shugaban kwamitin hulda da jama’a na rundunar Yansandan Akungba, Prince Rasheed Ajimo ya bayyana lamarin a matsayin mai muni, don haka ya yi kira a fara bincike, haka zalika shi ma kaakakin hukumar, Tee-leo Ikoro ya tabbatar da cewa sun kaddamar da bincike game da lamarin.

A wani labarin kuma, gungun miyagu yan bindiga sun tare babbar hanyar Birnin Gwari zuwa cikin garin Kaduna inda suka bude ma matafiya wuta, suka kashe na kashewa, suka sace na sacea sa’annan suka raunata wasu da dama.

Yan bindigan sun kai hare haren ne da yammacin ranakun Asabar da Lahadi na makon da ya gabata, inda ta dace daga cikin wadanda aka yi garkuwa dasu akwai dalibai da suka zana jarabawar JAMB a Kaduna, suna hanyarsa ta komawa gida a Birnin Gwari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel