Yan Bindiga Sun Shiga Masallaci Sun Dauke Masallata Ana Sallar Dare a Jihar Arewa

Yan Bindiga Sun Shiga Masallaci Sun Dauke Masallata Ana Sallar Dare a Jihar Arewa

  • 'Yan bindiga sun kai sabon farmaki Gusau, babban birnin jihar Zamfara yayin da Musulmi suke tsakiyar yin sallar Tahajjud
  • An ruwaito cewa an kai harin a ranar Talata, kuma 'yan bindigar sun kutsa cikin Masallacin inda suka yi awon gaba da masallata da dama
  • Harin na ranar Talata shi ne na kusa-kusan nan da 'yan bindiga ke kai wa masallata yayin da suke ibada a cikin Masallaci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gusau, jihar Zamfara - A ranar Talata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wani masallaci da ke unguwar Samaru bayan ofishin NEPA a garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da masallata.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kashe dumbin 'yan bindiga a jihohi 2 na Arewa, sun lalata sansaninsu

Rundunar 'yan sanda ba ta yi magana akan harin da aka kai Zamfara ba
Yan bindiga sun sace masallata da dama a Gusau yayin sallar Tahajjud. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Yan bindiga sun kai hari a Gusau

Jaridar Daily Trust ta gano cewa an kai harin ne a lokacin da Musulunci ke gudanar da sallar dare da aka fi sani da Tahajjud.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tahajjud wata Sallah ce ta musamman da Musulmi ke gudanar wa a kowanne kwanaki 10 na karshen watan Ramadan.

Harin na ranar Talata shi ne na kusa-kusan nan da 'yan bindiga ke kai wa masallata yayin da suke ibada a cikin Masallaci.

Hare-haren 'yan bindiga kan masallata

Sai dai har yanzu rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ba ta ce uffan kan harin ba, kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

A karshen watan Fabrairu, akalla masallata 40 ne 'yan bindiga suka sace a wani Masallaci da da ke Tsafe, jihar Zamfara.

An ruwaito cewa 'yan bindigar sun ajiye baburansu a bayan gari, suka badda kamanni yayin da suka shiga garin.

Kara karanta wannan

APC ta dauki zafi kan sharrin da aka yi wa Matawalle, ta gargadi PDP a Zamfara

Watan da ya gabata ma 'yan bindiga sun afka karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna inda suka kashe masallata biyu.

'Yan bindiga sun kashe masallata a Katsina

A wani labarin kuma, 'yan bindiga sun kai farmaki kan wasu masallata a jihar Katsina, inda suka kashe akalla mutane uku da jikkata wasu.

Legit Hausa ta ruwaito cewa 'yan bindigar sun kai harin ne a dai dai lokacin da mutane ken gudanar da sallar Isha'i a daren Alhamis, 16 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.