Gwamnatin Kano Ta Sallami Wasu Ma'aikata Daga Bakin Aiki, Ta Fadi Laifinsu

Gwamnatin Kano Ta Sallami Wasu Ma'aikata Daga Bakin Aiki, Ta Fadi Laifinsu

  • Rashin gaskiyar wasu ma'aikatan lafiya mutum uku ya jawo sun rasa aikinsu a jihar Kano bayan asirinsu ya tonu
  • Hukumar kula da asibitocin jihar ce ta ɗauki wannan matakin bayan ta same su dumu-dumu da laifin cin zalin marasa lafiya
  • Wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran hukumar ta fitar, ta tabbatar da korar ma'aikatan tare da dakatar da wasu guda uku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Hukumar kula da asibitocin jihar Kano ta kori ma'aikatan babban asibitin Kabo guda uku da dakatar da wasu guda uku bisa zargin cin zalin marasa lafiya.

Babban sakataren hukumar, Dakta Mansur Nagoda shi ne ya amince da hakan bayan ya kai ziyarar bazata a asibitin.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Uba da dansa sun yi taron dangi, sun yiwa matar makwabcinsu duban mutuwa a Ogun

Gwamnatin Kano ta kori ma'aikata
Gwamnatin Kano ta kori ma'aikatan lafiya kan cin zalin marasa lafiya Hoto: @KyusufAbba
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ta samu daga kakakin hukumar, Samira Suleiman, a ranar Litinin, 1 ga watan Afirilun 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane laifi ma'aikatan suka yi?

A cewar sanarwar ma'aikata uku na ɓangaren 'X-ray' an same su suna karɓar N12,000 domin yin 'X-ray', a maimakon N2,000 sannan ba wata takarda da ke nuna shaidar an biya kuɗin.

Wannan cin zalin da suke yi ya sanya asibitin yake yin ƙasa da 'X-ray' guda 10 a cikin sati ɗaya duk da cewa akwai kayan aikin kuma suna yin aiki yadda ya dace, rahoton jaridar PM News ya tabbatar.

Hakan ya sanya babban sakataren hukumar ya amince da korar ma'aikatan saboda cin zalin marasa lafiya da suke yi.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Haka kuma babban sakataren hukumar ya amince da dakatar da ma'aji, mai binciken kuɗi da shugaban sashen gwaje-gwaje saboda sayar da kayan yin gwajin cutar HIV da gwamnatin jiha ta ba asibitin kyauta.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta faɗi ranar da za a kammala ɗaukar sababbin ma'aikata a hukumar FFS

"An kuma umurcesu da su bayyana gaban hukumar domin ɗaukar matakin ladabtarwa."

Babban sakataren hukumar ya kuma sha alwashin hukunta duk ma'aikacin da aka samu yana aikata rashin gaskiya, domin hakan ya zama darasi ga saura.

An dakatar da naɗin sarauta a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta dakatar da naɗin Salisu Ado Bayero a matsayin Hakimin masarautar Bichi.

Gwamnatin ta umurci masarautar dakatar da bikin naɗin ne ta hannun wata sanarwa da kwamishinan ma'aikatar ƙananan hukumomi ya fitar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng