Ayyukan da Annabi Muhammad Ke Yawaita Yi a Kwanaki 10 Na Karshen Ramadan

Ayyukan da Annabi Muhammad Ke Yawaita Yi a Kwanaki 10 Na Karshen Ramadan

A yayin da azumin Ramadan na shekarar 1445 ya kai kwanaki 20, akwai bukatar mu waiwayi muhimman ayyukan da Annabi Muhammad (S.W.A) yake aikatawa a kwanaki 10 na karshe.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Goni Abubakar Sa'idu, malami daga jihar Katsina, a zantawarsa da Legit Hausa, ya bayyana cewa manzon Allah kan nunnunka ibada a kwanaki goma na karshen Ramadan.

A cewar malamin, an so Musulmi ya rabauta da samun wani lokaci mai daraja a karshen Ramadan, wanda ke yaye talauci duniya da lahira.

Malamin addini ya yi magana kan ayyukan da Annabi ke yi a karshen Ramadan
Daga manyan ayyukan da Annabi ke yi a kwanakin karshe na Ramadan akwai sallar dare. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ayyukan da Annabi ke yi a karshen Ramadan:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Kisan 'Yan Sanda a Delta: An kame mutum da ake zargi da yiwa jami'ai kisan gilla

Goni Sa'idu ya zayyana wasu muhimman ayyukan ibada da Annabi Muhammad yake yi a kwanaki goma na karshen Ramadan.

"Akwai bukatar Musulmi su yi koyi da manzon Allah a wadannan ayyukan ibada, domin samun arziki duniya da lahira."

- A cewar Goni Sa'idu.

Sallolin dare (Kiyamul Laili)

Malamin ya fara da cewa a kwanaki 20 na farkon Ramadan, Annabi kan yi sallolin dare ne yana bacci yana farkawa, har zuwa alfijir.

"Sai dai idan aka shiga kwanaki goma na karshe, manzon Allah yana raya dukkanin dare ba tare da yin bacci ba.
"Saboda muhimmancin kwanakin, manzon Allah kan tashi iyalansa daga bacci domin su yi ibada a dararen goma na karshen watan."

Neman arziki duniya da lahira

Goni Sa'idu ya ci gaba da cewa manzon Allah ya kwadaitar da al'ummarsa a kan neman dacewa da wasu lokuta masu daraja a kwanakin shekara.

"Idan mutum ya yi dace da wannan lokaci, to har abada ba zai lalace ba, zai samu arziki duniya da lahira.

Kara karanta wannan

2027: Tinubu ya bayyana hanyar da ƴan adawa za su iya tsige shi daga mulki

"Manzon Allah ya ce idan har mutum ya rabauta da wadannan lokuta, to tsiya da lalacewa ba za su taba samun mutum ba, sai tarin arziki na har abada."

- A cewar Goni Sa'idu.

Neman daren Lailatul Kadri

Malamin ya yi bayani kan muhimmancin yin ibada a dararen goma na karshen Ramadan domin dacewa da daren Lailatul Kadri.

A cewar Goni Sa'idu:

"Daren Lailatul Kadri kan zo ne a cikin kwanakin 'Mara', ma'ana kwana na 21, 23, 25, 27 ko 29 kamar yadda yazo a Hadisin manzon Allah (S.A.W).
"Allah a cikin Al-Kur'ani ya nuna cewa daren Lailatul Kadri shi me mafi alkairi a kan watanni 1000. Hakan na nufin dacewa da ibada a ranar, kamar yin ibadar shekaru 83 ne."

Yin ibadar I'itikafi

Goni Sa'idu, ya ce daga cikin ibadojin da manzon Allah yake yi kuma ya kwadaitar ayi shi ne shiga I'itikafi, ma'ana Musulmi ya zauna a masallaci yana ibada ba yankewa.

Kara karanta wannan

Babu hannu na a kashe sojojin Najeriya, Sarkin Delta da ya mika kansa ga 'yan sanda

Ya ce ana fara I'itikafi ne a kwanaki goma na karshen Ramadan, kuma hatta matan manzon Allah na yin I'itikafi, wanda ya nuna muhimmancin ibadar.

Sai dai malamin ya ce I'itikafi ba farilla bane ba, ibada ce wacce aka kwadaitar ayi domin neman dacewa da arziki duniya da lahira.

Yawaita addu'a a da sadaka

A cewar Goni Sa'idu, ana so Musulmi su dage da yin addu'o'i a kwanaki goma na karshen Ramadan, kamar yadda Allah (S.W.A) ya yi umarni a cikin Al-Kur'ani.

"Baya ga yawaita yin addu'o'i, ibada ta gaba ita ce yawaita yin sadaka. Ita sadaka tun daga farkon Ramadan ladarta ke kara nunkuwa.
"Abu mai muhimmanci shi ne sadaka ta ciyar da mai azumi, domin mutum zai samu ladar azumin wanda ya ciyar ba tare da an tauye ladar wanda aka ciyar ba."

- A cewar Goni Sa'idu.

A karshe, malamin ya shawarci al'ummar Musulmi da su dage da yin zikiri a kwanakin karshe na Ramadan, domin samun tsira da alkairi duniya da lahira.

Kara karanta wannan

Jerin manyan jami'an tsaro da bincike 5 da aka taɓa tuhuma kan saɓa doka

Jihohin da suka ba da tallafi Hajji

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa akalla gwamnoni 5 ne suka bayar da tallafin kudi ga maniyyata aikin Hajjin bana a jihohinsu.

Wannan na zuwa ne bayan da hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ta sanar da karin N1.9m ga maniyyata aikin Hajjin, lamarin da ya jawo cece kuce.

Baya ga gwamnatin tarayya da ya bayar da tallafi mai tsoka domin rage wa mahajjatan kasar kudaden da aka kara, jihohi ma sun yi nasu kokarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.