Goron Ramadan: Falalar daren Lailatul Qadr a wannan wata
– Manzon Allah yayi albishir da daren Laylatul Qadr a wannan wata
– An kuma yi kira a nemi daren a cikin goman karshe na watan azumi
– Wannan dare ya fi alheri a kan ibada na watanni dubu guda
Ana sa ran ganin daren nan mai albarka a cikin ‘yan kwanakin nan. Ba shakka daren Laylatul Qadr na nan cikin kwanaki goma na karshe. Ibada a wannan dare dai yana gaba da ibadar shekaru akalla 84
Manzon Allah SAW ya tabbatar da cewa za a dace da daren nan na Laylatul Qadr mai albarka a cikin ‘yan kwanakin nan na 10 na karshen watan Ramadan inda ake kasafin duk wani alheri a shekarar.
KU KARANTA: Arewacin Najeriya sun ce sun wuce gori
Ibada a cikin daren kamar yadda ya zo a Al-kur’ani cikin Suratul Qadr ya zarce ibada har na watanni dubu wanda idan aka lissafa zai bada kusan shekaru 84. Manzon Allah ya nemi a lalubi daren a cikin kwanaki na mara watau daren 21, 23, 25, 27 da kuma daren azumi na 29.
Haka kuma yayin da ake azumin watan Ramadan yana daga cikin ayyukan lada shiga I’itikafi watau kebawa a Masallaci ba a wani aiki face salloli da karatun Al-kur’ani mai girma a wannan lokaci.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Garin su Nnamdi Kani ya zama babban birnin Mahajjata
Asali: Legit.ng