Hadimi Ya Fadi Boyayyun Halaye da Sunan da Aka Radawa Shugaba Tinubu a Ofis

Hadimi Ya Fadi Boyayyun Halaye da Sunan da Aka Radawa Shugaba Tinubu a Ofis

  • Ajuri Ngelale ya bayyana halaye da dabi’un mai gidansa wanda ba kowa ya sani ba sai mutanen da ke zagaye da shi
  • Hadimin shugaban kasar ya ce Bola Ahmed Tinubu bai barci sosai, sannan da wuri yake tashi domin ya cigaba da aiki
  • Cif Ngelale ya ce Mai girma Bola Tinubu aiki yake yi babu dare ko rana saboda ya iya shawo kan matsalolin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Ajuri Ngelale ya bayyana mai gidansa a matsayin wanda bai gajiya da aiki, ya dage tukuru wajen kawo gyara a Najeriya.

Mai magana da yawun shugaban kasar ya Bola Ahmed Tinubu aiki yake yi dare da rana domin inganta halin da al’umma suke ciki.

Bola Tinubu
Bola Tinubu bai barci sosai a Aso Villa a cewar Ajuri Ngelale Hoto: @AjuriNgelale
Asali: Twitter

Ajuri Ngelale ya yabi Tinubu @72

Hadimin shugaban Najeriyan ya yi wannan bayani ne a lokacin da aka yi wata hira ta musamman da shi a tashar Channels a jiya.

Kara karanta wannan

Tinubu @ 72: Yadda aka taya Shugaban kasa murnar zagayowar ranar haihuwarsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ajuri Ngelale ya jinjinawa shugaba Bola Tinubu yayin da ya cika shekara 72 da haihuwa.

Shugaba Bola Tinubu bai barci da kyau

"Mutumin nan jakin aiki ne, shiyasa wasun mu da ke ofis mu ke yin ba’a, muna kiransa ‘shugaba ba barci’"
"Saboda har wasunmu da ke aiki da shi ba mu samun isasshen barci a dalilin haka."
"Ina tunani ‘yan Najeriya sun fahimta cewa tun lokacinsa a Legas, mutumin nan ya kan tashi a wasu bakin lokaci yana duba tituna, yana ganin ayyuka, ya tabbatar da ma’aikata sun zo ofis a kan lokaci."

- Ajuri Ngelale

Bayan Tinubu bai barci da wuri, mai taimaka masan ya ce da wuri yake tashi daga gado, ya ce jama’a ba su yi zaben tumun dare ba.

Tinubu jagora ne mai sauraron mutane

Daga cikin halin Mai girma Tinubu na kirki kamar yadda The Cable ta rahoto Ngalale yana cewa shi ne mutum ne mai sauraran mutane.

Kara karanta wannan

Abin da Bola Tinubu ya faɗawa manyan Malamai da Sarakuna a wurin buɗa baki a Aso Villa

Idan za ka shafe mintuna 30 ka na magana, hadimin ya ce shugaban kasa zai saurara, kuma zai yi nazarin abin da mutane ke fada.

Mai magana da yawun shugaban ya ce ba kowa ya san wannan ba sai na kusa da shi.

Nadin mukamai a gwamnatin Tinubu

Kamar dai Muhammadu Buhari, kun samu labari ana zargin shugaba Bola Tinubu yana fifita mutanensa wajen yin nadin mukamai.

‘Ya ‘yan shugabannin APC suna rike da mukamai, haka zalika Olufemi Akinyelure da mahaifinsa da ya samu kujera a kamfanin NNPCL.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng