“Wayyo Albashi Na”: Daga Ba Matarsa Ta Yi Cefane da Katin Kudinsa, Miji Ya Tashi Babu Anini a Asusu

“Wayyo Albashi Na”: Daga Ba Matarsa Ta Yi Cefane da Katin Kudinsa, Miji Ya Tashi Babu Anini a Asusu

  • Wani dan Najeriya da ya ce ya bai wa matarsa katin ATM dinsa domin ta yi cefaneya nuna kayan da ta saya da kudin
  • Matar ta yi siyayyar kayan abinci da yawa da gida zai bukata, amma mutumin ya ce albashinsa ya kare daga cefane daya
  • Ya yada hoton kayan a Facebook, inda ya haifar da cece-kuce da musayar ra'ayi daga mazan aure da suka fuskanci irin wannan

Bayan karban albashinsa, wani dan Najeriya ya baiwa matarsa katin ATM dinsa domin ta yi masu siyayya kayan abinci.

Sai dai, mutumin mai suna Israel Obinna Ugwu ya ce albashinsa ya kare saboda siyayyar da matarsa ta yi mai yawa.

Ya saka wani hoto a kafar Facebook don nuna irin kayan abincin da matarsa ta dawo dasu daga kasuwa a matsayin siyayya.

Kara karanta wannan

APC ta dauki zafi kan sharrin da aka yi wa Matawalle, ta gargadi PDP a Zamfara

Mutumin da cefane ya girgiza shi
Cefane ya girgiza wani dan Najeriya a Facebook | Hoto: Israel Obinna Ugwu
Asali: Facebook

Matar ta sayi kayan abinci na jarirai kamar su taliyar Indomie da wasu abubuwa masu muhimmanci na jin dadin iyali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya rubuta:

"Albashi na ya kare?! Ah! Me yasa na baiwa matar nan ATM dina?"

Hoton da kalamansa sun jawo cece-kuce a tsakanin abokansa da masu bibiyarsa a Facebook. Wasu sun taya shi murna domin har ya iya samarwa iyalansa abinci.

Martanin jama'a a Facebook jab cefanen da aka yi

Sodiq Sonko Amidu ya ce:

"Ba kai kace daga sati na biyu na wani wata za a biya albashin a kamfaninku ba?"

Chinazom Umeorji ya yi dariya yace:

"Kun kashe miliyoyin Naira a nan fa. Wannan kunzugun yaran kadai ya kusan #950,000 kuma ina ganin katon taliyar yara."

Peace Mbaneme ya ce:

"Shi kenan ka fara kirga albashi na gaba."

Vincent Onah Jude ya ce:

Kara karanta wannan

Hajjin bana: Sanata ya dauki zafi kan karin kudin kujera, ya fadawa Tinubu abin da zai yi

"Kunzugun yara shi ne kamar buhun shinkafa?"

Debbie Ojochenemi Ugwu ya ce:

"Wadancan kananan abubuwan sun kai 50k"

Khaleel Nasir Kiru yace:

"Zan zo gidanku."

Promise Ihezie ya ce:

"Ya kamata a bincike ku."

Cefane na kokarin kashe aure

A wani labarin kuma, wata matar aure, Basirat Ajayi, ta bayyana wa wata kotun da ke Mapo a Ibadan yadda mijinta, Ajayi Babatunde ke ba ta ita da ‘ya’yansu uku Naira 200 zuwa 500 a matsayin kudin cefane a kullum.

Basirat, wacce ‘yar kasuwa ce, ta ce mijin nata dan buguwa ne da ke shan taba kuma ya kwankwadi barasa kafin ya dawo gida da dare, Daily Trust ta ruwaito.

Ta ce surukarta ta kan yi mata fada, ta kara da cewa duk dangin mijinta suna da mugun hali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.