In ka bar min N2000 kudin cefane shawarma zanci, wata tsaleliyar beb ta ja kunnen samari da masu gida

In ka bar min N2000 kudin cefane shawarma zanci, wata tsaleliyar beb ta ja kunnen samari da masu gida

- Tsaleliyar yarinya tace ba wani batun biyayya, kawai samari su saki kudi

- Toseen taje shafin ta na Twita ne ta caccaki maza kan kwauro

- Tace N2000 bata iya ciyar da gida

In ka bar min N2000 kudin cefane shawarma zanci, wata tsaleliyar beb ta ja kunnen samari da masu gida
In ka bar min N2000 kudin cefane shawarma zanci, wata tsaleliyar beb ta ja kunnen samari da masu gida
Asali: Twitter

A lokacin da ake matsin tattalin arziki a kasar nan, musamman ta Buhariyya, da ma kuma wahalar miji, budurwa tsaleliya ta ce sam da sake, yadda ake daukar mata kamar ababen sayarwa, dole a fara sakin hannu.

A cewar Toseen dai, ko menene sai dai a kira ta, amma ita kam, naira 2000 babu abun da zata yi mata a gidan aure, in banda ta sayi Shawarma ta cinye abarta, maimakon wai ayi cefane a ci duk gida.

A gidaje da yawa dai, musamman a arewa, Shawarma sai an yi albashi, inda cefane ake yi aci abinci sosai a gida, shinkafa da miya har da nama.

DUBA WANNAN: Kabilun Yarabawa sun kasu kan Buhari da Atiku

Ana yi wa mace mai iya tattalin arzikin gida kallon babu yadda za'a yi ta rasa miji, inda kuma ake kallon wadda bata girki a matsayin mabarnaciya.

Ita kau Toseen, alawar mata, tace ko a jikinta, sai dai ta rasa mijin, amma N2000 kudin shawarma ne, ko indomie, babu batun mai gida ya dawo yaga tuwo a kwano.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng