Shugaba Tinubu Ya Fadi Abin da 'Yan Najeriya Suka Yi Wanda Ya Cancanci Yabo

Shugaba Tinubu Ya Fadi Abin da 'Yan Najeriya Suka Yi Wanda Ya Cancanci Yabo

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed ya nuna jin daɗinsa kan haƙuri da juriyar da ƴan Najeriya suka nuna kan gwamnatinsa
  • Shugaban ƙasan ya yi nuni da cewa haƙurin da suka yi ya fara haifar da ɗa mai ido a ƙasar nan
  • Ya buƙace su da su ƙara sadaukarwa kan wacce suke yi domin ganin an samu ci gaba mai ɗorewa a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - A yayin bikin Easter na bana, Shugaba Bola Tinubu ya yabawa ƴan Najeriya bisa hakurin da suka yi a ƴan watannin da suka gabata kan gwamnatinsa.

Shugaban ƙasan ya ce sadaukarwar da ƴan Najeriya suka yi ta fara haifar da ɗa mai ido, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu na bayar da tallafin N30,000? Gaskiya ta bayyana

Tinubu ya yabawa 'yan Najeriya
Shugaba Tinubu ya yabawa 'yan Najeriya kan hakuri da gwamnatinsa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Sai dai, yana son su ci gaba da nuna haƙura da juriya domin ganin ƙasar nan ta samu ci gaba da haɗin kan da ake buƙata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya tabbatarwa ƴan ƙasar nan cewa Najeriya za ta yi nasara kan ƙalubalen da take fuskanta a halin yanzu.

Me Tinubu ya ce ga ƴan Najeriya?

Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale, ya jaddada cewa gwamnatin ta duƙufa wajen cimma wannan manufa, rahoton jaridar Independent ya tabbatar.

A kalamansa:

"Shugaba Bola Tinubu ya bi sahun mabiya addinin Kirista don tunawa da Ista, wani muhimmin lokaci da kuma bikin tunawa da nasarar rayuwa kan mutuwa.
"Shugaba Tinubu ya lura cewa sadaukarwar da Yesu Kiristi ya yi ga bil’adama, darasi ne mai muhimmanci ga shugabanni da dukkan ƴan Najeriya da su jajirce wajen rashin son kai da nuna tausayi, da tsayin daka wajen neman ƙasa mai haɗin kai, zaman lafiya da wadata.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fusata kan ayyukan masu garkuwa da mutane, ya gadi matakin dauka a kansu

"Shugaban ƙasan ya kuma yabawa ƴan Najeriya bisa irin sadaukarwar da suka yi a cikin ƴan watannin da suka gabata domin al’ummar ƙasar ta samu hanyar farfaɗowa da kuma ci gaba mai ɗorewa.
"Yana mai tabbatar musu da cewa irin haƙurin da suka shuka ya fara tsirowa kuma za a samu ci gaba mai ɗorewa, sannan cikin ɗan ƙanƙanin lokaci zai samar da ƴaƴa masu yawa."

Tinubu ya ba ƴan adawa shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba ƴan adawa shawara kan yadda ƴan adawa za su iya raba shi da kujerarsa.

Tinubu ya yi musu nuni da cewa dole ne su jira zaɓe mai zuwa domin bin hanyar da kundin tsarin mulki ya tanada wajen kawar da shi daga kan mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng