2027: Tinubu Ya Bayyana Hanyar da Ƴan Adawa Za Su Iya Tsige Shi Daga Mulki

2027: Tinubu Ya Bayyana Hanyar da Ƴan Adawa Za Su Iya Tsige Shi Daga Mulki

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga ‘yan Najeriya da ke adawa da gwamnatinsa da su jira har zuwa zabe mai zuwa don tsige shi
  • Shugaban ya aike da wannan sakon ne a ranar Alhamis, a lokacin da yake tattaunawa da sarakunan gargajiya da na addini a Abuja
  • Tinubu ya bukaci malamai da sarakunan gargajiya da su kasance masu yi wa kasa addu'a da yada muhimmancin zaman lafiya ga al'umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan hanyoyin da kundin tsarin mulkin kasar ya shimfida na tsige zababbun shugabanni daga karagar mulki, ciki har da shi kansa.

Kara karanta wannan

Abin da Bola Tinubu ya faɗawa manyan Malamai da Sarakuna a wurin buɗa baki a Aso Villa

Bola Tinubu ya fadi hanyar tsige shugaba daga mulki
Tinubu ya shawarci ‘yan Najeriya da su jira zuwa zaben 2027 domin tsige shi daga mulki. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Tinubu ya yi magana ne hakan a lokacin buda baki na Ramadan tare da sarakunan gargajiya da malaman addini a fadar gwamnati a ranar Alhamis, kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

"Ku jira 2027 ku tsige shugaba" - Tinubu

Shugaban kasar ya yi nuni da cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

''Eh, fadin cewa wannan shugaban bai iya mulki ba dai dai ne. Sai dai dole ku jira har zuwa zabe na gaba don canza shi, amma kada ku la'anci kasar ku, domin kasa ce mai albarka."

Shugaban kasar wanda ya cika shekaru 72 a ranar Juma’a, 29 ga watan Maris, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa a shirye take ta magance kalubalen da kasar ke fuskanta a halin yanzu.

"Ka yi hattara" - Tinubu ya gargadi malamai

Jaridar Premium Times ta rahoto shugaban ya kuma bukaci shugabannin gargajiya da na addini da su guji bata sunan kasa a hudubobin da suke yi wa mabiyansu.

Kara karanta wannan

Ana daf da buda baki, Buhari ya tura sako ga Tinubu, ya yi masa ruwan addu'o'i

Ya bukaci shuwagabannin gargajiya da na addini da su kulla alaka mai karfi da gwamnati domin dakile ayyukan ta’addanci, ‘yan fashi, garkuwa da mutane da sauran laifuffuka a kasar nan.

"Soyayyar al'umma tana hannunku, ku yi wa kasarmu addu'a. Ku tarbiyantar da yaran mu. Wa’azin da muke yi a coci da masallatai yana da muhimmanci, domin haka kar mu rinka aibata kasarmu."

@72: Buhari ya aika sako ga Tinubu

A wani labarin, tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya aika muhimmin sako ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a yayin da ya cika shekara 72.

Buhari ya jinjinawa Tinubu kan yadda ya ce ya dakile matsaloli da yawa da Najeriya ke fuskanta tare da yi masa fatan samun ci gaba mai dorewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.