Dogo Giɗe Ya Mutu a Wani Asibiti a Sokoto? an Samu Karin Bayani Kan Lamarin
- Yayin da ake ta yaɗa jita-jitar mutuwar dan ta'adda, Dogo Giɗe, Legit Hausa ta yi bincike kan labarin mutuwarsa
- A jiya ne aka yi ta haɗa labarin cewa hatsabibin ɗan bindiga ya mutu bayan sojoji sun bude masa wuta a jihar Sokoto
- Har ila yau, an yaɗa cewa Giɗe ya mutu ne a wani asibiti a Sokoto, sai dai asibitin sun nesanta kansu da ba shi kulawa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Sokoto - A jiya Laraba 27 ga watan Maris an yi yadawa a kafofin sadarwa cewa hatsabibin ɗan bindiga, Dogo Giɗe ya mutu.
An yaɗa cewa dan bindiga ya mutu ne yayin da yake karɓar kulawa a wani asibiti mai zaman kansa a jihar Sokoto, cewar Nigerian Voice.
Asibiti sun yi martani kan jita-jitar a Sokoto
Sai dai hukumomin asibitin mai suna Reliance sun karyata cewa an kawo Dogo Giɗe asibitin domin kula da raunuka da ya samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana zargin sojoji ne suka farmaki dan ta'addan inda ya samu raunuka da dama a jikinsa da ya yi ajalinsa, cewar Daily Trust.
Dogo Giɗe dai shi ne ya addabi jihohin Zamfara da Sokoto da Katsina da Neja da Kebbi da jihar Kaduna da ke yankin Arewa.
Binciken Legit Hausa kan labarin
Sai dai Legit Hausa ta yi bincike kan gaskiyar wannan labari na kisan kasurgumin dan ta'adda da ya addabi al'umma.
A bincike da Legit Hausa ta yi babu wata sanarwa daga rundunar sojojin kasar kan wannan labari wanda ita ce ya kamata ta fara fitar da sanarwa kan mutuwar Giɗe.
Har ila yau, babu wata kafar yada labarai mai inganci da ta tabbatar da faruwar hakan ko kuma wata majiya mai karfi.
A binciken da Legit Hausa ta yi ta gano wani hoto da ake yadawa cewa shi ne Dogo Giɗe wanda wasu mutane suka musanta cewa hoton Giɗe ne.
A wata wallafa da wani ya yi a shafin Facebook ya ce asalin hoton da ake yaɗawa ba Dogo Giɗe ba ne, ya ce wani ne mai suna Dan Asabe daga jihar Kaduna da ya yi hatsari ya mutu.
Martanin rundunar 'yan sanda a Sokoto
Har ila yau, kakakin rundunar 'yan sanda a Sokoto, ASP Ahmed Rufai ya ce ba shi da labarin mutuwar shi ma a kafafen sadarwa ya ke gani.
Rufai ya yi alkawarin ba da cikakken bayani da zarar ya samu wani tabbaci kan labarin mutuwar Dogo Giɗe.
Sojoji sun yi ajalin hatsabibin ɗan bindiga
Kun ji cewa rundunar sojojin Nigeriya ta yi nasarar hallaka kasurgumin dan bindiga a jihar Zamfara.
Rundunar ta sanar da hallaka Junaidu Fasagora da mayaƙansa da dama yayin wani hari da ta kai.
Asali: Legit.ng