Fitaccen Malamin Addini a Arewa Ya Tona Manyan Mutanen da Ke Haɗa Kai da Ƴan Bindiga
- Malamin cocin Katolika a Sakkwato ya ce jami'an gwamnatin tarayya sun san manyan ƴan Najeriya da ke da hannu a ayyukan ƴan bindiga
- Bishof Matthew Kukah ya buƙaci gwamnatin tarayya a karƙashin jagorancin Bola Tinubu ta gaggauta ɗaukar mataki kan waɗannan mutane
- A cewarsa, akwai mutanen da suka fito suka yi ikirarin sun san wurin da ƴan bindiga suke zaune, don haka ya kamata a kamo su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Sokoto - Babban malamin cocin katolika na jihar Sakkwato, Bishof Matthew Kukah, ya tona asirin wasu manyan mutane da ke haɗa baki da ƴan bindiga.
Malamin cocin ya yi kira ga gwamnatin tarayya karkashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta karkata akalarta kan manyan mutanen da ke haɗa kai da ƴan ta'adda.
Kukah ya yi ikirarin cewa manyan ƙusoshin gwamnatin tarayya sun san ƴan Najeriya da ke haɗa kai da ƴan bindigar da ke sace ɗalibai domin neman kuɗin fansa a Arewa maso Yamma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwana nan rundunar sojojin Najeriya ta ceto ɗaliban da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su daga makarantar firamare da sakandire da ke Kuriga a jihar Kaduna.
Bayan samun wannan nasara, rundunar ta miƙa daliban hannun Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Da yake magana game da tabarbarewar matsalar tsaro a kasar nan musamman a Arewa, Bishof Kukah ya bukaci gwamnati ta dauki matakin gaggawa.
Wane mataki ya kamata gwamnati ta ɗauka?
A wata hira da ya yi da Channels tv, fitaccen malamin cocin ya ce:
"Sashin masu tattara bayanan sirri na da cikakken sani game da manyan ‘yan Najeriya da ke da alaƙa ta kusa da miyagun ƴan bindiga.
"A bayyane yake cewa gwamnatin tarayya a matakin koli ta san abin da ke faruwa. Aƙalla ƴan leƙen asirin gwamnati sun san wani abu.
“Akwai manyan ‘yan Najeriya da suka fito fili suka bayyana cewa sun fi mu saninsu, ina ganin ya kamata gwamnati ta zaƙulo masu ikirarin sun san wurin da ƴan bindiga suke, da masu haɗa kai da su."
Kukah ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya tana da karfin ikon da za ta zaƙulo waɗannan masu ikirarin sun san abin da ke faruwa kuma ta ɗauki mataki.
Da gaske an yi garkuwa da matar gwamna?
A wani rahoton na daban wani rubutu da aka wallafa a Facebook ya yi iƙirarin cewa an ɗauke uwar gidan gwamnan jihar Ribas, Lady Valerie Siminalayi Fubara.
Wani shafin binciken gaskiya ya gano ainihin abin da ya auku kuma ya wallafa rahoton ranar Talata, 26 ga watan Maris, 2024.
Asali: Legit.ng