Tinubu Zai Halarci Jana’izar Sojojin da Aka Kashe a Delta? Fadar Shugaban Ƙasa Ta Magantu
- Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu zai halarci jana'izar sojojin da aka kashe a jihar Delta
- Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, ya ce Tinubu ya damu matuka kan lamarin
- A cewar Onanuga, wannan shi ne karo na farko a cikin shekaru goma da shugaban kasar Najeriya zai halarci irin wannan taro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
FCT, Abuja – Shugaban kasa Bola Tinubu zai halarci jana’izar sojojin Najeriya da aka kashe a yankin Okuama da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.
Wasu ‘yan bindiga ne suka kashe sojojin a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris.
Tinubu zai karya tarihin shekara 10
Bayo Onanuga, mai ba da shawara na musamman kan yada labarai ga Shugaba Tinubu ya tabbatar da halartar shugaban kasar a cikin wani sakon X da ya fitar a shafinsa @aonanuga1956.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Onanuga ya ce wannan ne karon farko cikin shekaru goma da shugaban Najeriya zai halarci jana'izar sojojin da aka rasa.
Ya ce shugaban da ya bar kan karagar mulki bai halarci irin wannan jana’izar har guda biyu ba a shekarar 2021 da 2018.
"Tinubu ya damu matuka" - Onanuga
Hadimin ya yi nuni da cewa shugaba Tinubu ya halarci bikin binne sojojin ya nuna cewa ya damu kuma yana buga misali ne ga 'yan baya domin su yi koyi.
“An tabbatar da cewa shugaban kasa Bola Tinubu zai halarci jana’izar sojojin Najeriya da wasu ‘yan bindiga suka kashe a ranar 14 ga watan Maris a yankin Okuama da ke jihar Delta.
"Wannan dai shi ne karon farko cikin shekaru goma da wani Shugaban Najeriya zai halarci irin wannan gagarumin biki, domin karrama dakarunmu da suka sadaukar da rayuwarsu domin kare kasarsu."
- A cewar sanarwar.
Abubuwa da suka shafi bikin binne sojoji
A wani rahoton, Legit Hausa ta tattaro bayanai kan abubuwa biyar da ya kamata ku sani game da jana'izar sojojin da aka kashe a Delta.
Kamar yadda hukumar sojin Najeriya ta sanar, za a gudanar da bikin binne sojojin ne a yau Laraba, 27 ga watan Maris, 2024
Asali: Legit.ng