Harin Moscow: Hotunan Pantami da Tsohon Minista Sun Dira Ofishin Jakadancin Rasha

Harin Moscow: Hotunan Pantami da Tsohon Minista Sun Dira Ofishin Jakadancin Rasha

  • Yayin da ake jimamin harin da 'yan ta'adda suka kai birnin Moscow, tsohon Minista Isa Ali Pantami ya tura sakon jaje
  • Farfesa Pantami ya samu rakiyar tsohon Ministan jiragen sama, Femi Fani-Kayode zuwa ofishin jakadancin Rasha a Abuja
  • Wannan ziyarar jaje na zuwa ne bayan kai hari da 'yan kungiyar ISIS suka yi a birnin da ya yi ajalin mutane 137

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon Ministan Sadarwa a Najeriya, Farfesa Isa Pantami ya tura sakon jaje kan harin 'yan ta'adda a Moscow.

Pantami ya mika sakon jajen ne bayan harin da aka kai a birnin Moscow na kasar Rasha da ya hallaka mutane 137.

Kara karanta wannan

Jerin manyan jami'an tsaro da bincike 5 da aka taɓa tuhuma kan saɓa doka

Hotunan ziyarar Pantami da tsohon Minista a ofishin jakadancin Rasha
Isa Pantami da Fani-Kayode sun kai ziyara ofishin jakadancin Rasha domin jajanta musu kan harin Moscow. Hoto: @realFFK.
Asali: Twitter

Dalilin kai ziyarar da Pantami ya yi?

Kungiyar ISIS ita ta dauki nayin kai harin yayin wani taro da ake yi a bayan garin birnin Moscow.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon Ministan ya samu rakiyar tsohon Minista, Femi Fani-Kayode zuwa ofishin jakadancin Rasha da ke Abuja.

Farfesa Pantami ya nuna damuwa kan wannan iftila'i inda ya jajantawa shugaban Rasha da al'ummar kasar.

"Muna tare da ku, a kullum muna tare da zaman lafiya da kuma adalci, muna fatan wannan shi ne zai zama na karshe."
"Zamu ci gaba da taya ku addu'a da kuma kasarmu da kuma fatan samun zaman lafiya a duniya baki daya."

- Isa Ali Pantami

Martanin Fani-Kayode kan harin

A bangarensa, tsohon Ministan jiragen sama, Fani-Kayode ya wallafa a shafinsa na X inda ya ce Najeriya ta sha fama da wannan matsalar a baya.

Kara karanta wannan

Gumi ya taka rawa wurin kubutar da dalibai 137 a Kaduna? Uba Sani ya fayyace gaskiya

"Mun fuskanci irin wannan masifa a kwanakin baya, muna jajanta muku har cikin zuciya a madadin miliyoyin 'yan Najeriya."
"Mun san irin rawar da kuke takawa wurin ci gaban kasarmu, muna baku tabbacin kasancewa da ku a wannan hali."

- Fani-Kayode

Pantami ya ba dalibar musabaka kyaututtuka

A baya, kun ji cewa tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami ya ba daliba Hajara Ibrahim Dan'azumi kyautar mota da kuma tallafin karatu.

Dalibar dai ita ce ta lashe gasar karatun Alkur'ani ta duniya da aka gudanar a watan Faburairu a kasar Jordan.

Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya ba ta kyautar N5m yayin da hukumar Alhazai ta ba ta kujerar makka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.