Yan Bindiga Sun Kai Hari Ana Shirin Shan Ruwa, Sun Tafka Ɓarna Tare da Sace Matan Aure a Arewa
- Yan bindiga sun tattara matan aure 12 da namiji ɗaya sun yi awon gaba da su a wani ƙauye da ke yankin karamar hukumar Dutsinma a Katsina
- Mazaunin yankin ya bayyana cewa maharan sun shiga ƙauyen ana dab da shan ruwa, sun kwashi dukiyoyi na miliyoyin kuɗi
- Har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar ƴan sanda ko gwamnatin jihar Katsina kan sabon harin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Ƴan bindiga sun yi garkuwa da matan aure 12 tare da namiji ɗaya yayin da suka shiga kauyen Kurechin Giye, yankin Maƙera a ƙaramar hukumar Dutsinma a Katsina.
Yayin wannan farmakin, ‘yan bindigar sun kwashe dukiyoyi na miliyoyin Naira na mazauna garin suka yi awon gaba da su.
Wani mazaunin kauyen da ya nemi a sakaya sunansa sabida tsaro ya shaidawa Channels tv cewa ƴan bindigan sun shiga kauyen ɗauke da mugayen makamai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutumin ya bayyana cewa maharan ɗauke da miyagun makamai sun mamaye ƙauyen ne da yammacin ranar Litinin gabanin a sha ruwa, inda suka aikata wannan ta'adi.
Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?
A cewarsa, yayin harin wanda ya shafe kusan sa'a guda ƴan bindiga na aikata abin da ransu ke so, babu wani jami'in tsaro da aka turo kawo ɗauki.
"Da zuwan maharan, suka ɗauki kunun gero da mutanen kauyen suka shirya domin buɗa baki, suka riƙa watsa wa ƙananan yara da mata, kana daga bisani suka yi awon gaba da dukiya ta miliyoyin Naira," in ji shi.
Har kawo yanzu da muke haɗa wannan rahoton babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar ƴan sanda ko gwamnatin jihar Katsina kan sabon harin.
Matsalar tsaron Katsina
Wannan dai shi ne na baya-bayan nan a cikin jerin hare-haren garkuwa da mutane a jihar Katsina da ke shiyyar Arewa maso Yamma.
Ko a kwanakin nan, ƴan bindiga sun kai farmaki ƙauyen Mai-Ruwa da ke yankin karamar hukumar Faskari a jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.
Katsina dai na ɗaya daga cikin jihohin da lamarin garkuwa da mutane da ayyukan ƴan bindiga ya fi kamari a Arewacin Najeriya.
Yan bindiga sun shiga Tsafe
A wani rahoton kuma kun ji cewa Ƴan bindiga sun kai hari hedkwatar ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, sun kashe dakaru 2 na rundunar ƴan sa'kai CPG.
Wani mazaunin garin ya bayyana cewa maharan sun yi yunƙurin sace ɗaliban kwalejin horar da malaman lafiya ta Tsafe amma ba su cimma nasara ba.
Asali: Legit.ng