Dan Bindiga Ya Wallafa Bidiyo a TikTok, Ya Nuna Ƙuɗin Fansa da Ya Tara, Mutane Sun Harzuƙa
Ƴan Najeriya sun harzuƙa kan yadda suka ga wasu ƴan bindiga suna wallafa bidiyo a TikTok, suna nuna irin kuɗaɗen fansa da suka tara, tare da makaman da suka mallaka.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
An ga makudan kudaden ne a wani faifan bidiyo da Zagazola Makama, fitaccen mai sharhi kan harkokin tsaro ya wallafa a shafinsa na X.
Makama, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ya ce shafin da ɗan bindigar ke amfani da shi a TikTok har ya tara mabiya sama da 3,000.
Dan bindiga ya fara TikTok
Ya yi nuni da cewa wasu daga cikin ƴan bindigar da suka nuna irin makaman da suka mallaka na sanye da kayan sojoji da na ƴan sanda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Makama ya ce:
"Akwai sama da mutane 3,000 da ke bibiyar shafin, wasu daga cikin ƴan bindigar da aka nuna suna dauke da makamai cikin shigar sojoji da ƴan sanda.
"Dandalin TikTok ya ba ƴan ta'adda damar cin karensu ba babbaka ta hanyar dora bidiyoyin ayyukan ta'addancinsu ba tare da kwaɓa ba."
Kalli bidiyon a nan kasa:
'Yan Najeriya sun harzuka kan bidiyon
Ƴan Najeriya da dama sun harzuƙa kan wannan lamari, inda wasu ke cewa:
@tundealuko, ya ce:
"Dan bindiga na da shafi a soshiyar midiya amma ba za a iya kama shi ba. Amma wani da ya wallafa bayani game da shugaban EFCC an kama shi a kasa da makonni 2."
@mobilisingniger:
"Abin ban haushi shi ne an dauki bidiyon kwanaki 3 da suka gabata. Akwai faifan bidiyo da yake nuna inda ya je karbar kudin fansar wanda suka tsare.”
@Sikowitz17:
"Idan da wani ne ya zagi IGP ko fadar shugaban kasa kuma ya aka sami bidiyon da ke nuna fuskarsa a TikTok ko Twitter, da an kama shi a cikin 'yan sa'o'i."
@obajemujnr:
"Jami'an tsaro na iya bin duk wanda ya kuskura ya zagi 'yan siyasa, amma ba za su iya bin diddigin 'yan bindiga da ke fantamawa a kan TikTok ba.
@aamowuN:
“A nan kakakin ‘yan sandan Najeriya ya bugi kirji a kan cewa zai iya gano duk wanda ya zagi ‘yan sanda a soshiyar midiya cikin 'yan mintuna amma ba zai iya gano ‘yan fashin da ke yawo a kafafen sada zumunta ba.
@Tsure1∅1:
"Waɗannan mutanen dabbobi ne. Kuna kiran sunan Allah don ku aikata ta'addanci, kuna kashe mutane, da fashi da makami saboda kuna dauke da bindigogi a hannunku.”
Zamfara: Bidiyon ɗan bindiga mai karɓar haraji
A wani labarin, Legit Hausa ta kawo maku rahoton cewa an kama wani shugaban ƴan bindiga da ya addabi yankin Zamfara.
An ruwaito cewa dan bindiga mai suna Ya'u Babban Ƙauye, yana karbar haraji daga al'ummar wasu kauyuka na jihar, musamman yankin Tsafe.
Asali: Legit.ng