Bauchi: Adadin Mutanen da Suka Mutu Wajen Rabon zakka Ya Harba, an Samu Jerin Sunaye
- Ya zuwa yanzu, an samu jerin sunaye 15 na mutanen da suka mutu a wajen turmutsitsin rabon Zakkar Ramadan a jihar Bauchi
- Jami'in da ke kula da maƙabartar Dungulbe da ke Bauchi, Yahaya Mohammed ya bayyana cewa sun rufe gawarwakin mutane 15
- Sai dai rundunar ƴan sandan jihar ta ce mutane bakwai ne kacal likitoci suka tabbatar masu sun mutu daga wannan turmutsitsi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Bauchi - Adadin wadanda suka mutu sakamakon turmutsitsin karbar zakka a watan Ramadan da wani AYM Shafa ya raba, ya karu zuwa mutane 15.
Jami'in makabarta ya fadi adadi
Sakataren makabartar Dungulbe da ke Bauchi Yahaya Mohammed ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa mutum 15.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yau (Litinin), sun kawo daya daga cikin gawawwakin, wata mace ban da gawawwakin (Lahadi) guda 14. Matar da aka binne 'yar yankin Jahun ce.
"Ya zuwa yanzu mun binne jimillar mutane 15 daga cikin wadanda turmutsitsin ya rutsa da su, ciki har da manya 12 da yara uku."
- In ji Mohammed.
Jerin sunayen mutane 15
Mohammed ya bayyana sunayen wadanda aka kashe kamar haka:
- Alti Abdullahi Digan Yaya, mai shekara 55
- Maryam Suleiman, mai shekara 12
- Nana Khadija Suleiman, 'yar shekara 7
- Aisha Ibrahim Kobi, mai shekara 43
- Maryam Shuaibu, mai shekaru 16
- Aishatu Usman, ‘yar shekara 13
- Hauwau Musa, Sabon Kaura, mai shekara 50
- Aishatu Saidu Khandahar, 55
- Amina Abdullahi, mai shekaru 40
- Umaimah Yahaya, 'yar shekara 13
- Sahura Abubakar, mai shekara 48
- Zainab Ahmad, 'yar shekara 12
- Isa Aliyu Zango, dan shekara 3
- Khadija Yahaya, 'yar shekara 5
'Yan sanda sun ba da nasu rahoton
Sai dai jaridar The Cable ta ruwaito cewa rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, ta tabbatar da mutuwar mutane hudu ne kawai a ranar Lahadin.
Amma daga bisani rundunar ta ce wasu mata uku da suka jikkata sun mutu daga baya, wanda ya kawo adadin zuwa bakwai.
“Zuwa lokacin da muka bayar da wannan rahoton, muna da bayanin sunayensu da adireshin mutane bakwai da muka tabbatar sun mutu a turmutsitsin."
- In ji jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Ahmed Wakili.
Sunayen mutane 7 daga 'yan sanda
Wakil ya bayyana sunayen wadanda suka mutu da suka hada da Aisha Usman mai shekaru 13; Sahura Abubakar, 55; Aisha Ibrahim Abubakar, 43 da Khadija Isah, 8.
Sauran sun hada da Maryam Suleiman mai shekaru 20; Maryam Shuaibu, 16; da Hassana Saidu mai shekaru 53.
Wakil ya kara da cewa, wadannan su ne adadin wadanda likitocin kiwon lafiya suka tabbatar wa rundunar cewa sun mutu.
Zakka: Yan sandan Bauchi sun magantu
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa rundunar ƴan sandan Bauchi ta yi magana kan mutanen da suka mutu a wajen taron karbar Zakka a jihar.
Mai magana da yawun rundunar na jihar Bauchi, Ahmed Wakil, ya ce akwai wadanda suka mutu a asibiti, yayin da wasu suka mutu a gida.
Asali: Legit.ng