Akwai Hannun Na Kusa da Buhari: Omokri Ya Fallasa Wadanda Suka Kubutar da Wakilin Binance
- Tsohon hadimin shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya fadi cewa akwai wadanda suka kubutar da wakilin Binance, Nadeem Anjarwalla
- Reno Omokri ya ce wasu da suka rike manyan mukamai a gwamnatin tsohon shugaba Muhammadu Buhari su ne silar kubutar Anjarwalla
- Wannan na zuwa ne bayan shugaban Binance din ya sulale daga inda aka kulle sa a Abuja yayin da ya je gudanar da ibada a masallaci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Mai fashin baki a kafofin sadarwa, Reno Omokri ya bayyana wadanda suka kitsa sulalewar shugaban kamfanin Binance, Nadeem Ajarwalla.
Omokri ya ce Anjarwalla ya samu taimako ne daga wasu manya a Najeriya da suka rike manyan mukamai a gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Su wanene ake zargi da tserewar Anjarwalla?
Ya ce wadannan masu matukar tasiri a kasar su na tsoron barazanar Anjarwalla zai tona musu asiri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Reno ya bayyana haka ne a shafinsa na X a yau Litinin 25 ga watan Maris inda ya ce masu gadinsa kawai ‘yan aike ne.
“Yan Najeriya ne kamar yadda gwamnan CBN, Yemi Cardoso ya fada suka batar da $25bn zuwa kasashen ketare za su kitsa tserewar Anjarwalla.”
“Mutane ne masu girma da karfin fada a ji ne suke da hannu saboda barazanar bankada sunayensu.”
- Reno Omokri
Dalilin zargin na hannun daman Buhari
Ya ce lokacin da Buhari ya goge manhajar X, ministansa a lokacin, Abubakar Malami yana da manhajar Kiripto a wayarsa kuma ya na hana mutane kasuwancin Kiripto.
Reno ya ce ta yaya za a yi tsammanin mutum irin wannan zai zauna har a tona masa asiri kan badakalar kudi a Kiripto.
Wannan na zuwa ne bayan daya daga cikin shugabannin Binance, Nadeem Anjarwalla da ke tsare ya sulale bayan ya je yin ibadah a masallaci sabda azumi.
Reno Omokri ya ba Obi shawara
Kun ji cewa Reno Omokri ya ba dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP, Peter Obi shawara kan yadda zai shawo kan Musulmai.
Omokri ya ce dole Obi ya ba al’ummar Musulmi hakuri saboda kalaman da ya yi a lokacin da ya neman zaben 2023.
Asali: Legit.ng