Sheikh Gumi Ya Shiga Sabuwar Matsala Kan Zargin Alaƙa da Ƴan Bindiga, Bayanai Sun Fito
- Ƙungiyar RUN ta caccaki fitaccen malamin nan, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi bisa zarginsa da shiga tsakani na ƴan ta'adda
- RUN ya bukaci hukumomin tsaron Najeriya da su maida hankali kan Sheikh Gumi, kuma ta sanya shi cikin waɗanda take nema ruwa a jallo
- Kungiyar ta bayyana dalilin da ya sa take ganin kama Sheikh Gumi yana da matuƙar muhimmanci yayin Najeriya ke fama da ƴan bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Wata ƙungiyar matasa masu tasowa domin haɗa kan Najeriya (RUN) ya caccaki fitaccen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi.
Ƙungiyar ta buƙaci hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta sanya sunan Sheikh Gumi a cikin jerin mutane sama da 90 da take nema ruwa a jallo bisa zargin hannu a ta'addanci.
Malam Gumi wanda ke zaune a Kaduna ya yi kaurin suna wajen nuna goyon bayansa ga ‘yan bindiga kuma ba tare da neman afuwa ba ya yi tayin tattaunawa da su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban RUN, Solomon Adodo, da sakataren ƙungiyar, Suleiman Musa, sun yi ƙira a damƙe Malam Gumi.
"Ya kamata a kama Gumi" - RUN
A rahoton Vanguard ranar Litinin, 25 ga watan Maris, 2024 ƙungiyar ta bayyana matsayarta na a kama Shehin Malamin kan kalaman da yake game da ƴan bindiga.
Kamar yadda Blueprint ta tattaro, ƙungiyar ta ce:
“Kalamansa da tayin zama mai shiga tsakani da ‘yan ta’adda, musamman bayan sace ‘yan makaranta sama da 280 daga Kuriga, ya nuna ainihin kalar sa.
“Muna kira ga babban hafsan tsaro ya maida hankali kan Gumi, ya sanya shi cikin wadanda ake nema ruwa a jallo.
"Kama shi na da matukar muhimmanci domin sanin cikakken alakarsa da waɗannan miyagun mutane, musamman a Kaduna.
“Saboda haka ya kamata hukumar DSS ta gaggauta cafke Gumi kafin ya jagoranci kai hari fadar shugaban kasa.”
Gwamnati ta musanta biyan kuɗin fansa
A wani rahoton na daban Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ko kwandala ba a biya da sunan kuɗin fansa ba yayin ceto ɗaliban makarantar Kuriga ta Kaduna.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al'umma, Mohammed Idris, ne ya sanar da haka a fadar shugaban ƙasa bayan taron FEC ranar Litinin.
Asali: Legit.ng