Tsadar Iskar Gas: Jigon APC Ya Bukaci Shugaba Tinubu Ya Tausayawa Talaka

Tsadar Iskar Gas: Jigon APC Ya Bukaci Shugaba Tinubu Ya Tausayawa Talaka

  • An buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed ya yi wani abin kan tashin gwauron zabi da farashin iskar gas ɗin girki ya yi
  • Wani jigo a jam'iyyar APC, Olatunbosun Oyintiloye, shi ne ya yi wannan kiran inda ya yi nuni da cewa yana neman fin ƙarfin talaka
  • Ya koka kan yadda duk da matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka, har yanzu farashin nasa ya ƙi ya sauka

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Osun - Olatunbosun Oyintiloye, jigo a jam’iyyar APC, ya roƙi Shugaba Bola Tinubu da ya samar da hanyoyin magance tsadar iskar gas ɗin girki a ƙasar nan.

Oyintiloye ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin Osogbo, babban birnin jihar Osun a ranar Lahadi, 24 ga watan Maris 2024, cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu Ta faɗi gaskiya kan biyan kuɗin fansa yayin ceto ɗaliban Kaduna

Farashin iskar gas ya yi tsada
An bukaci Tinubu ya yi wani abu kan tsadar iskar gas (An yi amfani da hoton ne kawai domin misali) Hoto: PixelCatchers, Kypros
Asali: Getty Images

'Dan siyasar ya bayyana cewa tsadar iskar gas ɗin girkin ta sanya ya koma sai wane da wane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce a yanzu haka farashin cika tulun gas mai nauyin kilogiram 12.5 ya kai N17,500 zuwa N18,000.

A cewarsa umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar ga masu samar da iskar gas na dakatar da fitar da shi zuwa ƙasashen waje bai haifar da ɗa mai ido ba.

Wace shawara Oyintiloye ya ba Tinubu?

Ya yi nuni da cewa yana da yaƙinin cewa Shugaba Tinubu zai yi wani abu a kai, domin yana sauraren koken mutanen da yake jagoranta, rahoton jaridar Daily Post ya tabbatar.

A kalamansa:

"Dole ne dukkan masu ruwa da tsaki su haɗa kai da shugaban ƙasa domin tunkarar ƙalubalen da ake fuskanta a masana'antar man fetur da iskar gas.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Atiku ya caccaki Tinubu, ya fadi hanyar kawo karshen matsalar

"Hauhawar farashin iskar gas na iya kasancewa sakamakon masu samar da shi suna fitar shi zuwa ƙasashen waje a ɓoye."

Ya ce yin amfani da gawayi da itace a matsayin madadin iskar gas na da illa ga muhalli da kuma ƙara jawo taɓarɓarewar sauyin yanayi.

Iskar gas: Gwamnati ta karya farashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta fara shirin rage farashin iskar gas ɗin girki a ƙasar nan.

Hakan ya faru ne yayin da farashin iskar gas ɗin girkin ya ƙaru sosai daga ƙasa da naira 500 kan ko wane kilogiram a shekarar 2018 zuwa naira 1,300.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng