Daya Daga Cikin Jami’an Binance da Aka Tsare a Abuja Ya Tsere Yayin da Ya Je Sallah
- An samu matsala bayan daya daga cikin shugabannin Binance da aka tsare a Najeriya ya tsere a ranar Juma’a 22 ga watan Maris
- Ana zargin Nadeem Anjarwalla ya tsere ne bayan ba shi damar zuwa masallaci domin gudanar da ibada saboda azumin da ake yi
- Wannan ya biyo bayan tsare shugabannin Binance din a Abuja kan wasu zarge-zarge da suka hada da kin biyan haraji a Najeriya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Daya daga cikin shugabannin kamfanin Binance da aka tsare a birnin Abuja, Nadeem Anjarwalla ya tsere.
An tsare Nadeem Anjarwalla ne a Najeriya kan zargin kin biyan haraji da kuma sauran laifuffuka a can kwanakin baya.
Yaushe jami'in Binance ya tsere daga Abuja?
Premium Times ta tattaro cewa Mista Anjarwalla mai shekaru 38 ya tsere ne a ranar Juma’a 22 ga watan Maris daga gidan da aka tsare shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matashin ya tsere ne bayan jami’an tsaron da ke kula da shi sun ba shi damar zuwa masallaci da ke kusa domin gudanar da ibada saboda watan azumi.
Wanda ake zargin an tabbatar ya tsere ne inda ya fice daga Abuja wurin amfani da wani jirgin saman Gabas ta Tsakiya.
Jami’an tsaro sun tabbatar da cewa su na kokarin binciko inda Anjarwalla nufa domin tabbatar da kamo shi zuwa Najeriya, cewar BusinessDay.
Mai ba da shawara ga Shugaba Tinubu kan tsaro, Nuhu Ribadu ya tabbatar da tserewar Anjarwalla.
Ribadu ya ce tuni suka kama wadanda ke da alhakin tsaron matashin inda ya ce an fara gudanar da bincike kan lamarin.
Binance: Martanin jami'in shige da fice
Wani jami’in shiga da fice ya ce wanda ake zargin ya fice ne da fasfo na kasar Kenya wanda kuma an sani yana dauke da fasfon Birtaniya.
Jami’in ya ce suna kokarin bincikar yadda ya samu fasfo din da ya fice daga Najeriya inda ya ce takardun kasar Birtaniya kadai ya ke da su.
Wata majiya ta ce an tsare su ne tare da ba su dukkan wata dama da suka hada da rike waya wanda ake zargin shi ne damar da Anjarwalla ya yi amfani da ita.
An cafke jami’in manhajar Binance
Kun ji cewa Gwamnatin Najeriya ta cafke jami'an kamfanin Binance guda biyu bayan sun shigo kasar domin tattaunawa.
Ana zargin jami’an ne kan kin biyan haraji da kamfaninsu ya ke yi ga Najeriya da kuma sauran laifuffuka da dama.
Asali: Legit.ng