Filato: An Shiga Tashin Hankali Bayan Sabon Rikici Ya Barke, Bayanai Sun Fito

Filato: An Shiga Tashin Hankali Bayan Sabon Rikici Ya Barke, Bayanai Sun Fito

  • An jikkata mutane da dama a wani rikici da ya ɓarke tsakanin wasu matasa da ba sa ga maciji da juna a ƙaramar hukumar Mikang ta jihar Filato
  • Mutane da dama sun jikkata a rikicin da ya fara a daren ranar Asabar 23 ga watan Maris, wanda ya kai har zuwa safiyar ranar Lahadi 24 ga watan Maris
  • Da yawa daga cikin waɗanda suka samu raunuka sakamakon rikicin an kai su asibiti domin kula da lafiyarsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ponglong, jihar Filato - An ƙona gidaje da dama tare da sace shanu a sakamakon wani ƙazamin rikici da ya barke tsakanin matasa a yankin Ponglong da ke gundumar Lalin, a ƙaramar hukumar Mikang, ta jihar Filato.

Kara karanta wannan

Halin da Najeriya ke ciki ya sa Tinubu ya hakura da bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito a ranar Lahadi, 24 ga watan Maris, rikicin a tsakanin matasan Motola da Taroh, ya faru ne a daren ranar Asabar, 23 ga watan Maris, a ƙaramar hukumar Mikang.

Sabon rikici ya barke a Filato
Sabon rikici a jihar Filato ya lakume rayuka da dama Hoto: Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta ce an kashe wasu mutane da dama yayin da wasu masu yawa suka samu raunuka daban-daban.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu mazauna yankin sun ƙara da cewa har yanzu ba su kai ga tantance adadin mutanen da suka mutu a sakamakon ɓarkewar rikicin ba.

Yadda sabon rikicin Filato ya auku

Shugaban riƙon ƙwarya na ƙaramar hukumar, Daniel Kungmi, ya ce rikicin ya fara a tsakanin mutane biyu, daga baya wasu fusatattun matasa suka shiga ciki.

A kalamansa:

"A cikin ɗan lokaci kaɗan, lamarin ya ta'azzara wanda ya kai ga ƙone gidaje da rumbunan hatsi.
"Wasu ɓata gari sun yi amfani da rikicin wajen satar shanu da sauran kayayyaki masu amfani."

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan ceto daliban da aka sace a Kaduna, ya sha sabon alwashi

Ya ƙara da cewa bayan samun labarin aukuwar rikicin, sun sanar da jami'an tsaro waɗanda suka garzaya yankin cikin gaggawa domin dawo da doka da oda.

Matashi ya halaka mahaifinsa a Filato

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Filato ta kama wani matashi mai suna, Joseph Yakubu, wanda ake zargi da kashe mahaifinsa, Yakubu Dalyop.

Ƴan sandan sun kama matashin ne bisa zargin ya buga wa mahaifinsa taɓarya, kuma daga ƙarshe rai ya yi halinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng