Hukumar NAHCON Ta Kara Kudin Zuwa Aikin Hajjin Bana Na Shekarar 2024

Hukumar NAHCON Ta Kara Kudin Zuwa Aikin Hajjin Bana Na Shekarar 2024

  • Hukumar kula da Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta ƙara kuɗin zuwa aikin hajjin bana a ƙasar Saudiyya da Naira 1,918,032.91
  • Mai magana da yawun hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta sanar da hakan, inda ta bayyana cewa hakan ya faru ne saboda tashin dala
  • Da farko dai an kayyade kuɗin aikin Hajjin bana a kan Naira miliyan 4.9, lamarin da ya sa masu ruwa da tsaki daban-daban suka yi kira ga gwamnati ta kawo ɗauki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta sanar da ƙarin kuɗin zuwa aikin hajjin bana a ƙasar Saudiyya na shekarar 1445 (2024).

Hukumar ta sanar da wa’adin ranar 28 ga watan Maris, 2024 ga maniyyata da su kammala biyan kuɗaɗensu.

Kara karanta wannan

Bayan an kubutar da dalibai 137, Gwamna Uba Sani ya fadi hakikanin adadin daliban da aka sace

NAHCON ta kara kudin hajjin bana
Hukumar NAHCON ta kara N1.9m a kudin hajjin bana Hoto: Getty/AHMAD AL-RUBAYE
Asali: Getty Images

Hukumar ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa a shafinta na X ɗauke da sa hannun mai magana da yawunta, Fatima Sanda Usara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙarin kuɗin na da alaƙa da matsalar canjin kuɗaɗen ƙasashen waje da ƙasar nan ke fama da shi, bayan faɗuwar darajar naira.

Hajji: Me zai faru da wanda ya biya?

Kuɗin zuwa aikin hajjin na bana wanda da farko ya kai Naira miliyan 4.9 ya ƙaru zuwa Naira miliyan 6.8, inda ake buƙatar ƙarin Naira miliyan 1.9 daga waɗanda suka riga suka biya kuɗin tun da farko.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Maniyyatan da suke son zuwa aikin aikin hajjin bana na 2024 ana shawartarsu da su biya ƙarin N1,918,032.91 daga nan zuwa ƙarfe 11:59 na daren ranar 28 ga watan Maris 2024.
"Hukumar za ta rufe karɓar kuɗaɗen daga ranar 28 ga watan Maris, inda daga nan babu sauran kuɗin da za a sake karɓa."

Kara karanta wannan

Bayanai sun fito kan yadda aka ceto daliban da aka sace a jihar Kaduna

Saudiyya ta hana Umrah sau biyu

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumomi a ƙasar Saudiyya sun sanar da hana Alhazai gudanar da aikin Umrah sau biyu a cikin watan azumin Ramadan.

Ma'aikatar aikin Hajji da Umrah wacce ta sanar da hakan ta yi nuni da cewa an ɗauki matakin ne domin rage cunkoson jama'a a lokacin azumi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng