An Shiga Sabuwar Matsala, Bashin da China, Faransa, India, Jamus da Japan Ke Bin Najeriya Ya Karu
- Bayanai daga ofishin kula da basuka na kasa ya nuna cewa, bashin da ake bin Najeriya na kasashen waje ya kai $42bn
- Ga kasashe, DMO ya ce kasar China da wasu kasashen duniya hudu na bin Najeriya bashin da ya kai $5bn
- Kamar yadda aka yi tsammani, Najeriya cikin bashin China da wasu kasashen duniya dumu-dumu ciki har da Faransa da Jamus
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Ofishin kula da bashi (DMO) ya sanar da cewa, adadin bashin da ake bin Najeriya ya zuwa watan Disamban 2023 ya kai $42.49bn.
Wannan na nuni da raguwar 1.53% ko kuma $664.03m idan aka kwatanta da $43,15 da ake bin Najeriya a matsayin bashin waje a watan Yunin 2023 kafin fara mulkin Tinubu.
Wannan sabon rahoto dai ya fito ne daga ofishin na DMO, wanda Legit Hausa ta dauka tare da bin diddiginsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fashin bakin bashin da ake bin Najeriya na waje
A cewar rahoton na DMO, bashin waje da ake bin Najeriya ya fito ne daga kasashe da bankuna da kungiyoyin waje daban-daban, daga ciki har da IMF, Bankin Duniya, masu zuba hannun jari da kasashe.
A bangaren da ya shafi kasashe, ana bin gwamnatin Najeriya bashin da bai gaza $5.95bn, kamar dai yadda ya bayyana a rahoton.
Wannan kari ne idan aka kwatanta da na watan Yunin 2023, inda kasashen waje ke bin Najeriya akalla bashin $5.51.
Idan aka hada, bashin da kasashen duniya ke bin Najeriya ya kai 14.02% na jumillar bashin ya zuwa watan Disamban 2023.
Ga jerin bashin da kasashe ke bin Najeriya
Kasashe | Yunin 2023 | Disamban 2023 | Sauyi a lokacin Tinubu |
China | $4.72bn | $5.16bn | $440m |
Faransa | $572.61m | $580.13m | $7.52m |
Japan | $57.18m | $58.33m | $1.15m |
India | $26.64m | $25.94m | $0.70m |
Jamus | $135.26m | $125.90m | $9.36m |
Gwamnati ta biya bashin da ake bin Najeriya
A wani labarin, Babban Bankin Najeriya (CBN) ta biya bashin $7bn da gwamnan bankin, Yemi Cardoso ya gada bayan shigarsa ofis a 2023 daga hannun Emefiele.
Daraktar yada labaran bankin, Hakama Sidi Ali ita ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Laraba 21 ga watan Maris.
An tabbatar da biyan dukkan basukan wanda ake ganin zai iya saka darajar Nairanan ba da dadewa ba.
Asali: Legit.ng