Lokaci Ya Yi: Babban Basarake a Arewacin Najeriya Ya Kwanta Dama

Lokaci Ya Yi: Babban Basarake a Arewacin Najeriya Ya Kwanta Dama

  • An sanar da rasuwar Oloro na masarautar Oro a jihar Kwara, Oba AbdulRafiu Olaniyi Ajiboye Oyelaran
  • Basaraken ya rasu ne a safiyar ranar Asabar 23 ga watan Maris bayan doguwar jinya da ta shafe sama da shekara guda yana fama da ita
  • Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya ce Oba Oyelaran mai son zaman lafiya ne kuma uba ne ga kowa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kwara - Allah ya yi wa Oloro na masarautar Oro da ke ƙaramar hukumar Irepodun a jihar Kwara, Oba AbdulRafiu Olaniyi Ajiboye Oyelaran rasuwa a safiyar ranar Asabar 23 ga watan Maris.

An tattaro cewa basaraken ya rasu ne yana da shekara 70, shekara guda bayan da aka bayyana rasuwarsa inda daga baya aka gano akwai sauran shan ruwansa.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba Kabir ya yi ƙus-ƙus da Ministan Tinubu da jigon APC a Kano, bayanai sun fito

Oba AbdulRafiu ya rasu
Oba AbdulRafiu Olaniyi ya rasu yana da shekara 70 Hoto: @/timeless_update
Asali: Twitter

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, Oba Oyelaran ya rasu ne sakamakon doguwar jinya da ta shafe sama da shekara guda yana fama da ita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abdulrahman ya yi ta'aziyya

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya bayyana marigayi sarkin a matsayin mai son zaman lafiya, uba ga kowa, kuma mutum mai kishin ci gaban masarautarsa.

Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Rafiu Ajakaye Abdulrazaq ya fitar.

Ya ce za a yi kewarsa saboda gaskiyarsa, da jajircewarsa wajen samar da zaman lafiya da haɗin kai, da nasarorin da ya samu.

Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya ba al’ummar masarautar Oro da iyalan Oba Oyelara ikon ci gaba da gudanar da ayyukansa na alheri.

Jaridar Tribune ta ce mai martaba Sarkin Ilorin kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Kwara, (Dr) Ibrahim Sulu-Gambari CFR, ya bayyana marigayi Oba Oyelaran a matsayin sarki mai kishin al’umma da ci gaban jama’a.

Kara karanta wannan

Shahararren mawaki a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya a yau Juma'a

A kalamansa:

"Sarki ne mai son zaman lafiya da jajircewa wajen kawo ci gaba a cikin al'ummarsa. Gaba ɗaya mambobin majalisar sarakunan jihar Kwara na yi wa gwamnati da al'ummar jihar ta'aziyyar wannan babban rashi."

Gwamna Bago ya yi babban rashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Mai sarautar gargajiya a yankin Dikko-Enagi, Alhaji Muhammad Egba Enagi ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 90.

Marigayin da aka fi sani da Sarkin Malami Nupe ya rasu ne a ranar Asabar 9 ga watan Maris.

Marigayin shi ne mahaifin Fatima Bago, matar gwamnan jihar Neja, Alhaji Mohammed Umaru Bago.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng