Hotunan Dan Hazikin Dan Najeriyan da Ya Kammala Digiri da Maki Mai Ban Mamaki, Ya Sha Kyautar Kudi
- Wani hazikin dan Najeriya, Takon Roland Osaji ya kammala karatunsa na digiri a jami'ar UNICAL, ya gama da sakamako mafi kyau
- Shugabar jami'ar UNICAL, Florence Obi ce ta dalibin lambar yabon dalibin da ya fi kowa kawo maki mai kyau a jami'ar
- A rahoton da muka tattara, an ce matashin ya tafi gida da kyautar zunzurutun kudin da bai gasa Naira miliyan 1 ba
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Jihar Cross River - Wani hazikin matashi dan Najeriya, Takon Roland Osaji ya ba da mamaki yayin da ya kammala digirinsa a jami'ar Calabar; UNICAL.
A cewar shugabar jami'ar UNICAL, Florence Obi, matashin ya samu maki 4.85 cikin 5 na na CGPA a tarihin karatunsa.
Dalinin UNICAL ya ci kyautar N1m
Daily Post ta ruwaito cewa, Roland na daga cikin dalibai sama da 10,117 da suka samu nasarar kammala digiri a jami'ar ta Kudancin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Don mutantawa da karfafa gwiwa, dalibin na tsangayar tarihi ya ci kyautar N1m daga kungiyar shugabancin dalibai ta SUG.
A bisa al'ada, SUG kan ware irin wadannan kudade ne domin karfafa gwiwar daliban da suka fi kowa kwazo a shekara.
Bayanin shugabar jami'a
Shugabar jami'ar ta ce:
"Roland Takon dan tsangayar tarihi da ilimin kasa da kasa (zangon 2021/2022 mai lambar shiga 18/032144145 ne zakakurin dalibi kuma hazikin shekara.)
"Yana da makin CGPA 4.85 a ma'aunin maki 5. Shi muke afaharin sanar da ya ci kyautar SUG ta Naira miliyan 1 na dalibi mafi kwazo na shekarar."
Wani daga cikin tsaffin daliban jami'ar, Samuel Imo ya godewa Roland bisa sanya 'yan tsagayar tarihi alfahari a wannan biki na yaye dalibai da aka yi.
Dalibin jami'a ya rushe tarihin ABU
A wani labarin kuma, kun ji yadda Mufid Sulaiman ya yi tarihi da makin da ya kai 4.96 a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.
An ruwaito cewa, dalibin ya rushe tarihin da aka jima ana riritawa na tsauri da rashin samun maki mafi girma a tsangayar.
'Yan Najeriya dai mutane ne masu fikira da ake samunsu da aikin alheri a bangarori da dama a duniya.
Asali: Legit.ng