A bar yan kabilar igbo idan ballewa suke so, ba za mu iya wani yaki ba: Dattawan Arewa

A bar yan kabilar igbo idan ballewa suke so, ba za mu iya wani yaki ba: Dattawan Arewa

-Yan kabilar ibo suna neman yancin kai, a kokarin su na ballewa daga Nigeria.

- Kasar da mukayi mata fafutuka bai kamata ace wata kabila na neman ballewa ba, a cewar Hakem baba Ahmed

- Dattawan arewa sun yanke shawaran indai manyan dattawan ibo sun aminta to rabuwa ya zama dole

Kungiyoyin 'yan asalin yankin Biafra (IPOB) da kungiyar fafutukar tabbatar da kasar Biyafara mai mulkin mallaka (MASSOB) suna yakin neman rabewar yankin kudu maso gabas daga Najeriya.

Nnamdi Kanu ne ya kirkiri kungiyar IPOB a shekarar 2012, yayin da RSh Ralph Uwazuruike ya kafa kungiyar MASSOB a shekarar 1999.

Da yake zantawa da manema labarai bayan wata ganawar sirri da aka yi a Abuja a ranar Litinin, Hakeem Baba-Ahmed, mai magana da yawun kungiyar, ya ce hargitsin da Ibo ke yi na ballewa ya fara yin yawa, yakara da cewa shugabannin kasar sun nuna goyon bayan wannan shawarar.

KU KARANTA: Amurka tayi Alla-wadai da haramta Tuwita a Najeriya da Buhari yayi

A bar yan kabilar igbo idan ballewa suke so, ba za mu iya wani yaki ba: Dattawan Arewa
A bar yan kabilar igbo idan ballewa suke so, ba za mu iya wani yaki ba: Dattawan Arewa Hoto: ChannelsTV
Asali: Twitter

KU DUBA: Buhari fa ko amfani da wayar Andriod bai iya ba ballantana Tuwita, Fayose

Baba-Ahmed ya bada shawaran cewa tsayawa kai da fata ganin cewa an dakatar da masu tada kayar baya akan abunda suke so bazai haifar da da mai ido ba sai ma kara tabarbarewar rashin tsaro a kasar.

“Kasan nan ta sha fama da mummunan yaki domin kiyaye kasar.Arewa ta biya dukkan hakkokinta a wannan yakin, wanda ta jima tana yi ta hanyoyi daban daban a tsawon tarihin kasar, " inji shi.

"A halin da muke ciki a yanzu, babu wani dan Najeriya da zai yi maraba da wani yaki don ganin kasar ta cigaba da zama tsinstiya madaurinki daya ”

“Taron ya cimma matsaya mai tsauri kan cewa idan goyon bayan ballewa a tsakanin Ibo ya yadu kamar yadda ake dubi dashi, sannan suma shugabannin Ibo anga nuna amincewarsu to ya kamata a ba kasa shawara kar ta yi kokarin hana ruwa gudu.

“Bai kyautuba ace yan kabilar Ibo ko wani dan Najeriya ya yi yunkurin barin kasar da dukkanmu muka yi wahala domin ganin ta ginu, kasar da kowa keda alhakin kawo mata sauyin alkairi."

Kungiyar ta yi gargadin cewa dole ne a daina kai hare-hare da kashe-kashen ‘yan arewa, ma’aikatan gwamnatin tarayya, da kuma lalata dukiyar kasa, ta kara da cewa dole ne a kamo wadanda ke da hannu a gurfanar da su.

Dattawan na arewa sun kuma kara da cewa har sai kabilar Ibo sun yanke shawara game da ko suna son ballewa ko kuma za su ci gaba da kasancewa a cikin Najeriya, doka na nan bata chanza ba, tunda gwamnatocin tarayya da na jihohi sune da alhakin tabbatar da doka da kuma kare hakin kowani dan kasa.

Sun kuma goyi bayan kiraye-kirayen da ake yi wa ‘yan arewa da ke fuskantar musgunawa da tashin hankali, da su wai wayo su dawo gida.

A bangare guda, Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta bayyana cewa Arewa ce ke haifar da rashin tsaro a yankin Kudu maso Gabashin kasar.

Hakan martani ne ga kalaman da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aliyu Wamakko, ya yi cewa shugabannin Ibo ne ke haifar da matsalar tsaro a yankin Kudu maso Gabas.

Sakatare-janar na kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Okechukwu Isiguzoro, ya bayyana kalaman na Wamakko a matsayin abin dariya, yana mai fadawa tsohon gwamnan cewa ya fara gyara rikicin Arewa kafin yin wani tsokaci game da Kudu Maso Gabas, jaridar Guardian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel