Rikicin Biyafara: A shirye muke wajen yakar sojojin Najeriya – Kungiyar IPOB

Rikicin Biyafara: A shirye muke wajen yakar sojojin Najeriya – Kungiyar IPOB

- Kungiyar tsaro na Biyafara (BNG) sun kaddamar da cewa a shirye suke su yaki sojojin Najeriy

- Hakan ya kasance ne sakamakon kaddamar da kungiyar da sojojin Najeriya sukayi a matsayin na yan ta’adda

- Kungiyar ta BNG sunce zasu kare mutanen kudu maso gabas daga ko wani hari

Jami’an tsaro na kungiyar Biyafara wanda aka fi sani da suna Biafra National Guard (BNG) sun bayyana cewa a shirye suke su yaki rundunar sojin Najeriya saboda dole su kare rayukan al’ummar kudu maso gabashin kasar.

Jami’an BNG sun bayyana hakan ne bayan sojoji sun kira kungiyar IPOB a matsayin kungiyar yan ta’adda.

Jami’an BNG sun ce rundunar sojin Najeriya ta dade ba ta yi abunda ta ga dama ba saboda su kan sai sun kare rayukar al’ummar kudu maso gabashin Najeriya.

Rikicin Biyafara: A shirye muke wajen yakar sojojin Najeriya – Kungiyar IPOB
Rikicin Biyafara: A shirye muke wajen yakar sojojin Najeriya – Kungiyar IPOB

Inda ta ce kiran kungiyar IPOB a matsayin kungiyar yan ta’adda ba wani abu bane izgili irin ta Gwamnatin kasar Najeriya, inda suka bayyana cewa kungiyar IPOB za ta dawo kan bakan ta nan ba da dadewa ba.

KU KARANTA KUMA: Abun da shugabanni yakamata su gaggauta yi game da Najeriya – Saraki

An samu labarin ne a cikin wani sanarwa da kakakin jami’an BNG, Major Nkuma, wanda ya turawa kafafen yada labarai na Daily Post inda ya bayyana cewa BNG ba kungiyar ta’addanci bane karawa da cewa, Gwamnatin Najeriya ta zanto abun dariya tunda har za ta sanar da cewa kungiyar IPOB, kungiyar ta’addanci ne.

A cikin sanarwan Sun tabbatarwa gwamnatin Najeriya da cewa dole su kare kan su don ba za su mika wuya ba har sai bayan mutuwar su kafin hakan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng