Gwamnatin Malam Dikko da Sojoji Sun Samu Gagarumar Nasara Kan Ƴan Bindiga a Watan Azumi
- Gwamnatin Malam Dikko Raɗda da haɗin guiwar sojojin sama sun ceto karin mutane 17 da aka yi garkuwa da su a dajin Jibia a jihar Katsina
- Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Dakta Nasiru Mu’azu Danmusa, ya ce gwamnatin ta bai wa tsaro fifiko fiye da komai
- Tun da farko, shugaban ƙaramar hukumar Jibia, Sabi'u Maitan, ya yabawa gwamnati tare da fatan ceto ragowar mutum 88 nan ba da jimawa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina tare da haɗin guiwar rundunar sojin saman Najeriya sun sake samun nasarar ceto mutum 17 da aka yi garkuwa da su.
Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, an ceto rukunin mutanen ne daga jejin Jibia wanda ke kan titin Jibia zuwa Ɓaure a jihar Katsina.
Wadanda aka ceto sun fito ne daga kauyen Karofi da ke karamar hukumar Jibia a jihar kuma sun hada da matan aure uku da ƙananan yara 14.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanai sun nuna cewa matan da ƙananan yaran da ba su wuce shekara biyar zuwa 10 a duniya ba, sun shafe kwanaki 15 a hannun ƴan bindiga.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Dakta Nasiru Mu’azu Danmusa ne ya tarbi mutanen da aka kubutar a madadin Gwamna Dikko Umaru Radɗa.
Wane matakai gwamnati ke ɗauka?
Danmusa ya kuma sanar da cewa gwamnatin Katsina karkashin Malam Dikko ta ɗauki lamarin tsaro da matuƙar muhimmanci domin zaman lafiya ya samu wurin zama a tsakanin al'umma.
Ya kuma tabbatar da kudirin gwamnatin jihar mai ci na kawo ƙarshen ‘yan ta’adda, inda ya kara da cewa tsaro shi ne abu na farko, na biyu, da na uku da gwamnatin ta sa a gaba.
Kwamishinan ya kuma bukaci mazauna jihar da su sanya gwamnati a cikin addu’o’insu na yau da kullum domin dawo da zaman lafiya a dukkan sassan Katsina.
Ɗanmusa ya ce:
"Gwamnatin jihar Katsina ta maida hankali wajen kare rayuka da dukiyoyin mazaunan jihar."
Ƴan bindiga na riƙe da mutum 88
Tun da farko a jawabinsa, shugaban karamar hukumar Jibia, Sabi’u Maitan, ya yabawa gwamnatin jihar da jami’an tsaro bisa wannan samame da nasarar ceto mutane.
Ya bayyana yaƙinin cewa nan ba da jimawa ba za a kubutar da sauran mutane 88 da ‘yan bindigan suka yi garkuwa da su.
Kwanaki uku da suka gabata ne gwamnatin Katsina ta tabbatar da cewa dakarun sojoji sun ceto mata 10 da ƙananan yara 6 a Maraban Kaigoran, The Cable ta ruwaito.
An sace fasinjojin motar KTSTA
Wani rahoto ya zo cewa ƴan bindiga sun tare motar bas mai ɗaukar fasinjoji 18 mallakin hukumar sufuri ta jihar Katsina, sun yi garkuwa da mutane da yawa.
Ganau sun bayyana cewa maharan sun tare motar ne a yankin ƙaramar hukumar Kankara ranar Alhamis, 2 ga watan Maris, 2024.
Asali: Legit.ng