Bola Tinubu Ya Kori Mutumin Buhari, Ya Naɗa Sabon Shugaban Hukumar Kula da Kayan Tarihi
- Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Mista Olugbile Holloway a matsayin sabon shugaban hukumar kula da gidajen tarihi ta ƙasa
- Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Alhamis, 21 ga watan Maris, 2024
- Holloway zai maye gurbin Farfesa Abba Tijani, wanda tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya naɗa a watan Augusta, 2020
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Mista Olugbile Holloway a matsayin darakta janar na hukumar kula da gidajen tarihi da kayan tarihi ta ƙasa.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Cif Ajuri Ngelale, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Alhamis, 21 ga watan Maris.

Kara karanta wannan
NEC: Gwamnoni 16 sun goyi bayan ƙirkiro ƴan sandan jihohi domin dawo da zaman lafiya

Asali: Facebook
Tinubu ya maye gurbin mutumin Buhari
Mista Holloway ya maye gurbin Farfesa Abba Tijani, wanda tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya naɗa ranar 26 ga watan Agusta, 2020.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya zama cikakken darakta janar/shugaban hukumar kula da gidajen tarihi na takwas a tarihi.
Babban mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin kafafen sada zumunta na zamani, Dada Olusegun, ya wallafa sanarwar wannan naɗi a shafinsa na manhajar X.
A cewar sanarwan, Mista Holloway ya karanci ilmin siyasa da hulɗar ƙasa da ƙasa a digirinsa na farko yayin da ya karanta harkokin kasuwannci a digiri na biyu.
Sanarwar ta ce:
"Shugaban ƙasa na fatan sabon darakta janar zai farfaɗo da wannan hukuma mai matukar muhimmanci da kuma tabbatar da tsaro, bunkasa da haɓaka al'adun Nijeriya iri daban-daban na zahiri da waɗanda ba a taɓa gani ba."
Wannan na zuwa mako ɗaya bayan Shugaba Tinubu ya naɗa Dakta Temitope Ilori a matsayin shugaban hukumar yaƙi da cutar kanjamau ta ƙasa (NACA).
CBN ya biyan bashin $7bn?
A wani rahoton na daban Saɓanin ikirarin CBN, kamfanonin jiragen sama na kasashen waje sun musanta cewa an biya su kuɗaɗensu da suka maƙale
Babban bankin Najeriya (CBN), a wata sanarwa, ya bayyana cewa ya biya waɗannan kuɗaɗe na kamfanonin da suka makale a Najeriya
Asali: Legit.ng