Sojoji Sun Kashe Hatsabibin Ɗan Bindiga da Ya Addabi Bayin Allah a Jihar Sakkwato
- Sojoji sun kashe wani ɗan bindiga mai hatsari da ke sanya kakin ƴan sanda yana yaudarar mutane a jihar Sakkwato
- Mai magana da yawun rundunar sojojin ƙasa, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya ce sojojin sun samu wannan nasara ne ranar Laraba
- Ya ce bayan wannan, sojoji sun halaka wani ɗan ta'adda a jihar Taraba tare da ƙwato nuggan makamai daga hannunsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Sokoto - Dakarun rundunar sojin Najeriya sun yi nasarar halaka hatsabibin ɗan bindiga mai haɗari wanda ke shigar ƴan sanda yana aikata ta'addanci a jihar Sakkwato.
Sojojin sun kuma lalata ma'ajiyar magungunan ƴan bindiga da wuraren kiwon lafiyarsu a wani samame da suka kai ranar Laraba 20 ga watan Maris, 2024.
Mai magana da yawun rundunar sojojin ƙasa, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ne ya bayyana haka a wata sanarwa a X a ranar Alhamis (yau), 21 ga watan Maris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Nwachukwu, dan ta’addan ya sha yin shiga a matsayin ɗan sanda wajen yaudara da yin garkuwa da mutane masu yawa da ba a san adadinsu ba.
Sojoji sun kashe wani a Taraba
Sanarwar wadda rundunar soji ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Alhamis ta ƙara da cewa:
"A wani samamen na daban da dakarun sojoji suka kai a jihar Taraba, sun yi nasarar kashe wani ɗan ta'adda a ƙauyen Kutoko da ke ƙaramar hukumar Takum a jihar."
"Baya ga haka, a samamen sojoji sun kuma kwato bindiga ƙirar AK-47 da Magazine ɗauke da alburusai huɗu na musamman masu nauyun 7.62mm."
Kakakin rundunar ya ƙara da cewa irin wannan hare-hare da sojoji ke kai wa na ƙara tabbatar da cewa rundunar sojin Najeriya ta shirya kakkaɓe duk wani nau'i na ta'addanci.
A cewarsa, wannan wani ɓangare ne na yunƙurin rundunar soji wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali sun samu gindin zama a tsakanin al'umma.
Sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci
A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya ta ayyana Tukur Mamu, ɗan jarida a Kaduna da wasu mutum 14 a matsayin masu ɗaukar nauyin ta'addanci a Najeriya.
Legit Hausa ta tattaro muku sunayen mutanen da gwamnati ke zargi suna angiza wa ƴan ta'adda kuɗaɗe, wanda ya ƙunshi kamfanoni da ƴan canji 6.
Asali: Legit.ng