Hukuncin da Za a Yanke Wa Iyayen da Yaransu Ba Sa Zuwa Makaranta a Najeriya
- Majalisar dattawa ta gabatar da kudurin hukunta iyayen da yaransu ba su zuwa makaranta a Najeriya
- Majalisar ta ce za a kafa kotunan tafi-da-gidanka domin yanke hukunci ga iyaye idan aka kama yaransu na gararamba a lokacin karatu
- Sanata Adebule Oluranti ne ya gabatar da bukatar yana mai nuna barazanar da rashin zuwan yara makaranta ke da ita ga tsaro a ƙasar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A ranar Laraba, majalisar dattawa ta gabatar da kudurin hukunta iyayen da suka yi watsi da ƴaƴansu tare da ƙin tura su makarantar boko.
Sanata Adebule Idiat Oluranti (Legas ta Yamma) ne ya gabatar da kudurin wanda ke nuna muhimmancin daƙile yawaitar yara marasa zuwa makaranta.
Hukuncin ɗauri na watanni 6 ga iyaye
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa majalisar dattawa ta kuma duba yiwuwar kafa kotunan tafi-da-gidanka da za su wajabta ilimin zamani a kan kowane yaro a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban majalisar, Godswill Akpabio, ya nemi gwamnoni da suyi amfani da dabarar da ya yi wajen shawo kan matsalar a lokacin yana gwamnan jihar Akwa Ibom.
Dabarar ita ce; yanke hukuncin dauri na watanni shida a kan iyaye ko iyayen rƙo da suka tura yaransu gona, aike ko talla alhalin lokacin yara na makaranta.
Illolin rashin tura yara makaranta
Da ya ke goyon bayan kudirin, Sanata Ahmed Lawan (APC, Yobe ta Arewa) ya ce akwai yara sama da miliyan 20 wadanda ba sa zuwa makaranta a Najeriya.
Lawan ya ce ya zama wajibi a shawo kan matsalar domin gudun ƙara tabarbarewar tsaro a nan gaba a ƙasar, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.
Shi ma mataimakin shugaban majalisar, Sanata Barau Jibrin (APC, Kano ta tsakiya), ya nuna damuwarsa kan cewa rashin tura yara makaranta ne ke kyankyasar ƴan ta'adda.
Direba ya mutu bayan ya dauko dalibai
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa, wani direba ya yanke jiki ya fadi yana tsaka da tuki a hanyar zuwa kai dalibai makaranta.
Mahukuntan jami'ar Ilorin da suka tabbatar da faruwar lamarin, sun ce direban mai suna Lukman ya mutu rike da sitiyari, lamarin da ya jefa daliban a tashin hankali.
Asali: Legit.ng