'Yan Bindiga Sun Kashe Manoma da Dama, Sun Tafka Mummunar Ɓarna Ana Azumi a Jihar Arewa
- Wasu ƴan bindiga sun kai mummunan farmaki kan manoma yayin da suke tsaka da aiki a gonakinsu a jihar Benuwai a ranar Talata
- Mazauna kauyen Onipi da ke ƙaramar hukumar Utukpo sun ce maharan sun kashe manoma biyu yayin da wasu da dama suka ji raunuka
- Kantoman Otukpo, Alfred Omakwu ya tabbatar da lamarin da cewa an kai waɗanda suka jikkata asibiti domin kula da lafiyarsu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - Rahotanni sun bayyana cewa wasu ƴan bindiga da ba a sani ba sun halaka manoma biyu tare da jikkata wasu da dama a jihar Benuwai.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, maharan sun yi ajalin manoman ne yayin da suka kai farmaki ƙauyen Onipi da ke ƙaramar hukumar Otukpo.
A cewar mazauna yankin, wasu manoman sun ji raunuka daban-daban a harin yayin da har yanzu ake neman wasu da suka ɓata a harin wanda ya faru da safiyar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun kuma bayyana cewa ƴan bindigan sun rutsa manoman ne yayin da suke tsaka da aiki a gonakinsu, suka tafka wannan mummunar ɓarna.
Ciyaman ya tabbatar da lamarin
Yayin hira ta wayar tarho da wakilin jaridar, shugaban ƙaramar hukumar Otukpo na riƙon kwarya, Alfred Oketa Omakwu, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Mista Omakwu ya ce mutane 12 ne suka jikkata yayin harin kuma tuni aka garzaya da su asibiti domin a yi musu magani.
Kantoman ƙaramar hukumar ya ƙara da cewa maharan sun ƙona wata Keke Napep da ta ɗauko doya.
A cewarsa, wannan shi ne karo na farko da miyagun ƴan bindiga suka kai hari kan mutane a kauyen Onipi, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, rundunar ƴan sandan jihar da gwamnatin Benuwai ba su ce komai game da sabon harin ba.
Yayin da aka tuntuɓi jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sandan Benuwai, SP Catherine Anene, ba ta ɗaga kiran waya ko amsa sakonnin tes kan lamarin ba.
Ƴan bindiga sun kai hari Zamfara
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun kai mummunan farmaki a kauyen Ɓaure da ke Zamfara, sun halaka masu azumi da dama.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya sanar da cewa maharan sun farmaki garin a kan babura akalla 30.
Asali: Legit.ng