Yadda Yajin Aiki SSANU/NASU Ya Jawo Silar Mutuwar Wani Dalibin Jami'a
- Jami’ar gwamnatin tarayya, da ke Oye-Ekiti, (FUOYE) ta zargi ƴan ƙungiyar SSANU/NASU da kasancewa silar mutuwar wani ɗalibin makarantar
- Mahukuntan FUOYE sun ce ɗalibin wanda yake fama da ciwon asma ya mutu ne saboda an kulle asibitin jami'ar
- Mataimakin shugaban jami'ar, Tajudeen Opoola, ya ce ƴan daba sun mamaye makarantar ne bayan da shugaban SSANU na jami'ar ya ba shugaban ƙungiyar na ƙasa bayanan ƙarya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Oye-Ekiti, jihar Ekiti - Hukumar gudanarwar jami’ar gwamnatin tarayya, da ke Oye-Ekiti (FUOYE) ta ce yajin aikin da ƙungiyar manyan ma'aikatan jami’o’in Najeriya (SSANU) da ƙungiyar NASU ke ci gaba da yi ya haddasa mutuwar wani ɗalibi.
Mataimakin shugaban jami'ar, Tajudeen Opoola, tare da wasu shugabannin jami'ar ne suka bayyana hakan ga manema labarai a ranar Talata, 19 ga watan Maris.
A cewar Opoola, ɗalibin mai ciwon asma ya mutu ne saboda ya kasa samun kulawa nan take sakamakon shiga yajin aikin da ƙungiyoyin suka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi nuni da cewa wasu jami’o’in ba a rufe su ba kamar FUOYE, wacce ƙungiyar SSANU ta sanya aka kulle, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.
Menene silar mutuwar ɗalibin jami'ar?
A kaƙamansa:
"Mun rasa wani ɗalibi da ya kamu da cutar asma saboda ba a iya kai shi asibitinmu ba. An kulle asibitin da kwaɗo. Gaskiya ne cewa ɗalibai suna hutu, amma ba duka suke zaune a cikin makaranta ba.
"Zai fi sauƙi ga ɗalibin a garzaya da shi zuwa asibitinmu domin samun kulawar gaggawa, amma ko ƙofar shiga jami’ar mu a kulle take."
Yajin-aikin SSANU/NASU a jami'ar EKSU
Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, Opoola ya ce a jami'ar jihar Ekiti (EKSU), ofisoshin ɓangaren gudanarwa da asibiti suna aiki kamar babu wani yajin aikin da ake yi.
Ya ce shugaban SSANU na jami'ar EKSU ya tura ƴan daba domin a kulle makarantar bayan shugaban ƙungiyar na jami'ar ya bada bayanan ƙarya cewa an yi masa dukan tsiya a jani'ar FUOYE.
Direban mota ya mutu a jami'ar Ilorin
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani direba ya rasa ransa yana tsaka da tuƙa ɗalibai zuwa harabar jami'ar Ilorin da ke jihar Kwara.
Direban dai ya rasu ne bayan ya yanke jiki ya faɗi, inda wani ɗalibi da ke a gaban motar ya samu ya tsayar da motar bayan ya fahimci abin da ya auku.
Asali: Legit.ng