'Yan Majalisar da Aka Dakatar a Zamfara Sun Garzaya Kotu, Sun Ambato Bukatunsu

'Yan Majalisar da Aka Dakatar a Zamfara Sun Garzaya Kotu, Sun Ambato Bukatunsu

  • Biyo bayan kokawa kan tauye musu haƙƙi da aka yi, dakatattun ƴan majalisar dokokin jihar Zamfara sun garzaya kotu
  • Ƴan majalisar su takwas sun shigar da ƙara kan kakakin majalisar da wasu mutum shida a gaban babbar kotun tarayya da ke Gusau
  • A ƙarar dai sun yi zargin cewa ana yunƙurin cafke su da tuhumarsu biyo bayan dakatarwar da aka yi musu daga aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ƴan majalisar dokokin jihar Zamfara guda takwas da aka dakatar, sun shigar da ƙara kan shugaban majalisar dokokin jihar, Bilyaminu Moriki, da wasu mutum shida a babbar kotun tarayya dake Gusau.

Dakatattun ƴan majalisar sun shigar da ƙarar ne, inda suke ƙalubalantar tauye musu haƙƙinsu da aka yi, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fallasa sunayen masu daukar nauyin ta'addanci, za ta dauki mataki

An kai karar kakakin majalisar dokokin Zamfara
'Yan majalisar da aka dakatar a Zamfara sun shigar da kara a kotu Hoto: Ebi Dressman
Asali: Facebook

Ƴan majalisar a ƙarar sun yi nuni da cewa an yi musu ƙwacen kadarorinsu ba bisa ƙa'ida ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su wa dakatattun ƴan majalisar ke ƙara?

Ƙarar dai an shigar da ita ne kan mutum bakwai da suka haɗa da, Antoni-Janar na jihar, kwamishinan shari’a, shugaban majalisar dokokin jihar, magatakardan majalisar, kwamishinan ƴan sanda na jihar da daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).

Alƙalin kotun, mai shari’a Aminu Bappa, ya amince da bukatar sannan ya ɗage ƙarar zuwa ranar 29 ga watan Afrilu domin sanar da waɗanda ake ƙarar, rahoton Daily Post ya tabbatar da haka.

Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala zaman kotun, lauyan dakatattun ƴan majalisar, Ibrahim Ali, ya buƙaci a sanya ranar sauraron ƙarar, domin samun damar sanar da sauran waɗanda ake ƙara.

Meyasa suka shigar da ƙarar?

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu: Kotu ta yi hukunci kan shari'ar shugaban kungiyar IPOB

A cewarsa, waɗanda ya ke karewa sun yi zargin cewa shugaban majalisar tare da haɗin bakin rundunar ƴan sanda da jami'an sibil difens (NSCDC) sun fara yunƙurin kama su tare da tuhumarsu.

Idan dai za a iya tunawa majalisar dokokin jihar a ƙarƙashin jagorancin kakakinta, ta dakatar da ƴan majalisar bisa zargin cewa sun saɓa dokokin kundin tsarin mulkin majalisar.

Ƴan majalisa na fuskantar barazanar kisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakatattun ƴan majalisar dokokin jihar Zamfara, sun bayyana cewa rayuwarsu na fuskantar barazana.

Ƴan majalisar sun yi zargin cewa ƴan daba na farautar rayuwarsu bayan sun fallasa yadda matsalar tsaro ta ta'azzara a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng