Rana Ta Ɓaci: Mutane Sun Kashe Wani Ɓarawo Yana Ƙoƙarin Satar Babur a Masallaci
- Rahotanni sun bayyana cewa wasu gungun fusatattaun mutane sun kashe wani ɓarawo yana ƙoƙarin satar babur a masallaci a jihar Bauchi
- An ruwaito cewa barawon ya yi yunkurin satar wani babur, lokacin da wani ya hango shi ya yi masa 'ihu barawo', inda aka rufe shi da duka
- Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Auwal Musa Mohammed, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin tare da kama masu laifin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa, yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Bauchi - Wasu fusatattun matasa sun lakada wa wani da ake zargin barawon babur dukan tsiya har lahira a garin Magama-Gumau da ke karamar hukumar Toro a jihar Bauchi.
Daily Trust ta ruwaito cewa mutane sun ankare da barawon ne da yammacin ranar 17 ga watan Maris, inda ya ke kokarin satar wani babur a kusa da wani masallaci.
Rana ta baci ga barawon babur
Majiyoyi sun bayyana cewa, an ga barawon ya yi amfani da karfi ya balle kwadon wani babur da aka ajiye tare da fara gungura shi zuwa wajen masallacin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai rana ta baci ga barawon bayan da mai babur din da ya hango shi daga cikin masallacin, ya fito a guje ya bi shi yana 'ihu barawo!'
Da ga jin ihun, sai mutane suka bi barawon suka kama shi duk da cewa ya yi jefar da babur din da ya sata a kokarin tserewa daga wurin.
Kowa ya watse bayan kashe barawo
Tribune Online ta ruwaito cewa, saboda ranar kasuwa ce, sai nan da nan jama'a suka taru da itatuwa da sauran kananun makamai suka yi ta dukan barawon har ya mutu.
Kafin jami’an ‘yan sanda su isa wurin, duka wadanda ke a wajen suka watse, kowa ya kama gabansa.
Daga baya ‘yan sandan sun dauki gawar tare da ajiye ta a dakin ajiye gawa na babban asibitin Toro.
Matakin da 'yan sanda suka dauka
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Ahmed Mohammed Wakil, kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito.
SP Wakil ya bayyana cewa da isar su wurin da lamarin ya faru, jami’an ‘yan sanda suka tarar da gungun mutane sun kona wanda ake zargin.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Auwal Musa Mohammed, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin tare da kama masu laifin.
Kano: Kotu ta garkame wani barawon babur
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa, wata kotu a jihar Kano ta yanke hukuncin zaman gidan yari na watanni tara ga wani barawon babur da aka kama a jihar.
Barawon babur din mai suna Bashir Sani Ungogo, an kama shi ne bayan ya shiga ma'aikatar filaye da safiyo ta jihar ya yi awon gaba da wani babur da kudinsa ya kai N350,000.
Asali: Legit.ng