Mutuwa Rigar Kowa: Fitaccen Furodusan Fina-Finai a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Mutuwa Rigar Kowa: Fitaccen Furodusan Fina-Finai a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Shahararren mai shirya fina-finai a masana'antar Nollywood, Cif Ikechukwu Nnadi, ya riga mu gidan gaskiya a Owerri, babban birnin jihar Imo
  • Marigayin wanda ya fi shahara da sunan Andy Best ya mutu ne bayan fama da dogowar jinya da wata cuta da ba a bayyana ba ranar Talata, 19 ga watan Maris
  • Jarumi mai riƙe da kambun gwarzon masana'antar Nollywood, Seun Oloketuyi, shi ne ya tabbatar da rasuwar a shafinsa na sada zumunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Owerri, jihar Imo - Fitaccen mai shirya fina-finai a masana'antar Nollywood, Cif Ikechukwu Nnadi, wanda aka fi sani da Andy Best ya mutu.

Rahotanni sun bayyana cewa Nnadi ya jima yana kwance yana fana da rashin lafiya na tsawon lokaci.

Kara karanta wannan

Sarki Charles III ya yi bankwana da duniya? Gaskiya ta bayyana

Andy Best.
Fitaccen Furodusan Nollywood, Andy Best ya mutu Hoto: Seun Oloketuyi
Asali: Instagram

Amma an tabbatar da cewa ya mutu a wani asibiti a Owerri, babban birnin jihar Imo ranar Litinin, 19 ga watan Maris, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai riƙe da kyautar gwarzon masana'antar Nollywood da ke kudancin Najeriya, Seun Oloketuyi, ne ya tabbatar da rasuwar a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Jarumin ya sanar da cewa Andy Best ya mutu ne a wani asibitin birnin Owerri yau Talata.

Ya ce:

“Andy Best, babban furodusa kuma mai talla a masana'antar Nollywood, ya mutu. An tabbatar da rai ya yi halinsa ne a wani asibiti a Owerri yau (Talata 19 ga watan Maris).

Taƙaitaccen bayani gane da marigayin

Nnadi ya fito ne daga kauyen Umunkwo da ke karamar hukumar Isiala Mbano a jihar Imo da ke shiyyar Kudu maso Gabashin Najeriya.

Har zuwa ƙarshen rayuwarsa, Andy Best ya kasance babban shugaban kamfanin shirya fina-finan Andy Best Production.

Kara karanta wannan

Cushe a kasafin kudi: Sanata ya tabbatar da karbar Naira biliyan 1 na ayyukan mazaba

Ya shirya fitattun fina-finai da dama, da suka hada da Lion of Africa, White Poison, My Father’s Cup da dai sauransu.

Ali Nuhu ya kama aiki gadan-gadan a NFC

A wani rahoton na daban kun ji cewa Sarki Ali Nuhu ya karɓi ragamar hukumar fina-finai ta Najeriya (NFC) a hukumance a Jos, babban birnin jihar Filato.

Yayin da ya kama aiki a matsayin MD na NFC, Ali Nuhu ya tabbatar wa mahalarta taron cewa ya shirya tsaf domin aiki tuƙuru da nufin inganta aikin hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262