Edo 2024: Abin da Shugaba Tinubu Ya Fadawa Ɗan Takarar Gwamnan APC, Okpebholo

Edo 2024: Abin da Shugaba Tinubu Ya Fadawa Ɗan Takarar Gwamnan APC, Okpebholo

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya miƙa tutar jam'iyyar APC ga ɗan dan takarar gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo
  • A yayin mika tutar a fadar shugaban kasa da ke Abuja, Tinubu ya ba Okpebola da abokin takararsa tabbacin goyon bayansa
  • Tinubu ya jaddada cewa jam'iyyar APC ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen ganin ta samu nasara a zaben gwamnan jihar Edo da za a yi watan Satumba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A ranar Litinin ne Shugaba Bola Tinubu, ya mika tutar jam’iyyar APC ga dan takarar gwamnan jihar Edo na jam’iyyar, Monday Okpebholo, da abokin takararsa, Dennis Idahosa.

A yayin gabatar da tutar a fadar Aso Villa da ke Abuja, shugaban ya bayyana fatansa na ganin jam’iyya mai mulki ta samu nasara a zaben da za a yi a Edo a watan Satumba.

Kara karanta wannan

Sarki Charles III ya yi bankwana da duniya? Gaskiya ta bayyana

Tinubu ya gana da dan takarar gwamnan APC na jihar Edo
Edo 2024: Tinubu ya mika tutar APC ga Monday Okpebholo, da abokin takararsa, Dennis Idahosa. Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Okpebholo: Tinubu ya nuna goyon bayansa

Da yake jawabi a wajen taron kamar yadda Channels TV ta ruwaito, shugaban ya yi alkawarin cewa jam'iyyar za ta tsaya tare da 'yan takarar "kamar bangon Gibraltar".

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Idan kuna farin ciki, muna farin ciki. Za mu yi aiki tukuru, kuma za mu tsaya tsayin daka tare da ku kamar bangon Gibraltar.
"Abin da zan iya tabbatar muku ke nan a yanzu. Jam’iyyar mu tana da girma, amma nasara ta fi komai girma kuma muna bukatar wannan nasarar."

- A cewar shugaban kasar.

Tinubu ya yabawa Adams Oshiomhole

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban kasar.

Shafin fadar shugaban kasa ya wallafa cewa Tinubu ya yabawa shugabannin jam’iyyar na Edo bisa kokarin da suke yi na samun nasarar ‘yan takara da jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya sake cin karo da babbar matsala kan takarar da yake nema karo na 2

Ya yabawa tsohon gwamnan jihar, Adams Oshiomhole, bisa kyakkyawan jagoranci.

Tinubu ya yi fatan APC ta yi nasara

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

“Ya mai girma sanata kuma mai rike da tutarmu, muna sa ku a gaba domin ku rike mana jam’iyyar da amana da kuma fatan samun nasara a gare mu.
"An bayyana ka da abokin takarar ka a matsayin jiga-jigai da suka san lagon siyasa, kuma wadanda ke yin aiki tukuru tare da shugabannin jam’iyya domin cimma nasara."

A nasa jawabin shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya jaddada cewa akwai hadin kai a jam’iyyar wanda zai basu damar samun nasara a zaben.

Rikici a jam'iyyar PDP kan zaben Edo

A wani labarin, jam'iyyar PDP a jihar Edo ta shiga wani sabon rikici biyo bayan tayar da tarzoma da Philip Shaibu ya yi akan lallai shi ne jam'iyyar za ta ba tikitin takarar gwamna.

Legit Hausa ta ruwaito cewa rikicin ya fara ne tun bayan da Shaibu ya ci zaben fidda gwani na jam'iyyar a wani tsagi na masu kada kuri'a, sai dai PDP ta ayyana wani daban a matsayin dan takararta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.