Gwamnan APC Ya Fitar da Maƙudan Kuɗi Domin Rabawa Talakawa Abinci Kyauta a Ramadan
- Mai Mala Buni ya amince da fitar da kuɗi Naira miliyan 100 domin ciyar da marasa galihu kowace rana a watan nan na Ramadan
- Kwamishinan addinai na jihar Yobe, Yusuf Umar, ne ya tabbatar da haka yayin da yake duba aikin raba kayan abinci ga masu girki da ƴan kwangila
- Ya shawarci waɗanda zasu yi aikin su ji tsoron Allah SWT, su ɗauki aikin a matsayin hanyar samun lada a wurin Allah a gobe ƙiyama
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Yobe - Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da kashe N100, 000, 000.00 domin ciyar da mabuƙata da marasa galihu 16, 800 a watan azumi.
Gwamna Mala Buni ya fitar da waɗannan makudan kuɗi har Naira miliyan 100 ne domin ciyar da mazauna jihar masu ƙaramin karfi a tsawon watan Ramadan.
Mutane za su koshi da Ramadan a Yobe
Kwamishinan ma'aikatar harkokin addinai da ɗa'a na jihar Yobe, Yusuf Umar ne ya bayyana haka a Damaturu, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Umar ya faɗi hakan ne yayin da yake rangadin duba rabon kayan abinci ga masu girki da waɗanda aka ba kwangilar aikin a babban birnin jihar Yobe.
Ya ce hakan na ɗaya daga cikin matakan da Gwamna Buni ya dauka na tabbatar da tallafi ya isa ga al’umma musamman marasa galihu a watan azumin Ramadan.
Yadda gwamnatin Yobe ta tsara ciyarwar Ramadan
Ya ce kawo yanzu gwamnati ta fadada cibiyoyin ciyar da abinci daga na farko 67 zuwa 84, inda kowace cibiya za a ciyar da akalla mutane 200 a kullum.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa, a shirin ciyar da maɓukata na watan Ramadan, gwamnatin Buni ta ware Naira miliyan 100, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Ya kara da cewa an raba dukkan kayan abinci da sauran kayan girki ga masu girkin da aka zaɓa da kuma ‘yan kwangila domin gudanar da aikin yadda ya kamata.
Jawabin Kwamishinan addinai na jihar Yobe
“Ina mai tabbatar muku da cewa za mu sa ido sosai kan yadda masu girki da ‘yan kwangilar ke gudanar da ayyukansu da nufin tabbatar da sun bi yarjejeniyar da suka rattabawa hannu da gwamnati.
"Wannan wata ne mai alfarma, watan da kowane musulmi ke son ribatar falalar Mahaliccinmu, don haka ya kamata ‘yan kwangila su dauki aikin ciyarwa a matsayin damar hidima ga jama'a domin samun lada a lahira.”
- Yusuf Umar.
Da muka zanta da wasu ƴan jihar Yobe sun yi farin ciki da yunkurin gwamnatin amma a cewarsu har yanzu ba amo ba labari.
Ahmad Tijjani ya shaidawa Legit Hausa cewa a kafafen yaɗa labarai suka ga labarin, amma har yanzun ba su ga komai a ƙasa ba.
"Na ga gwamnoni da dama suna wannan ciyarwa, babu shakka abu ne mai kyau amma mu a nan Yobe shiru kake ji, ana ta yaɗa labarai amma ba haka abun yake ba," in ji shi.
Aliyu Muhammad ya ce har zuwa ranar 9 ga watan Ramdan, ba a fara shirin ba a yankinsa, amma ya yi fatan cewa Allah ya sa nan gaba gwamnatin ta aiwatar da abin da take faɗa.
Ramadan: An sace babura a Masallaci a Abuja
A wani rahoton na daban Wasu ɓarayi sun sace baburan mutane yayin da ake tsaka da sallar tarawihi da daren ranar Asabar a Paso da ke birnin Abuja.
Wani mazaunin yankin, Mika'il Abdulsalam, ya ce tun farkon Ramadan ake zuwa da baburan masallacin amma sai ranar asabar aka ɗauke su.
Asali: Legit.ng