'Yan Ta'adda Sun Kai Sabon Farmaki a Jihar Arewa, Sun Sace Mutum 87
- Ƴan ta'adda sun sake kai harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna a yankin Arewa maso Yamma na Najeriya
- A yayin harin wanda suka kai cikin dare a ƙauyen Kajuru-Station, ƴan ta'addan sun yi garkuwa da mutane 87
- Miyagun waɗanda ke ɗauke da makamai sun kuma fasa shaguna tare da sace kayan abinci da sauran kayayyaki masu amfani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Ƴan ta'adda sun sace mutum 87 a ƙauyen Kajuru-Station, da ke ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.
Ƴan ta'addan sun farmaki ƙauyen ne a daren ranar Lahadi, 17 ga watan Maris, 2024, cewar rahoton jaridar The Nation.
Harin na zuwa ne kwanaki biyu bayan ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutum 16 a ƙauyen Dogon-Noma da ke a ƙaramar hukumar ta Kajuru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴan ta'addan suka kai harin
Wani mamba a ƙungiyar matasan Kajuru-Station, Harisu Dari, ya tabbatar wa da jaridar The Punch aukuwar lamarin a ranar Litinin a Kaduna.
Harisu ya ce ƴan ta’addan sun kuma fasa wasu shaguna inda suka yi awon gaba da kayan abinci da sauran kayayyaki.
Ya ce sun mamaye ƙauyen ne da misalin ƙarfe 10:00 na dare.
Harisu ya bayyana cewa har yanzu ƴan ta'addan ba su kira waya ba kan mutanen da suka sacen.
A kalamansa:
Har zuwa lokacin da na ziyarci ƙauyen a safiyar yau Litinin, babu jami’an tsaro da za su taimaka wajen kwantar da hankulan mazauna ƙauyen.
"Mutanen ƙauyen suna cikin baƙin ciki game da abin da ke faruwa. Ya kamata gwamnati ta sake dabarar tunkarar waɗannan ƴan ta’addan"
Me hukumomi suka ce kan lamarin?
Legit Hausa ta yi ƙoƙarin tuntuɓar kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.
Sai dai, har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ta wayarsa ba.
An sheƙe shugaban ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro na ƴan sa-kai sun samu nasarar sheƙe ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga a jihar Katsina.
Ƴan sa-kan sun sheƙe Kachalla Maude ne bayan sun yi masa kwanton ɓauna a ƙauyen Garin Rinji da ke ƙaramar hukumar Batsari ta jihar.
Asali: Legit.ng