Hukumomin Saudiyya Sun Dakatar da Yin Umrah Sau Biyu a Cikin Watan Ramadana
- Kasar Saudiyya ta hana yin Umrah sau biyu a cikin watan Ramadana, ta bayyana dalilai masu karfi kan haka
- A lokacin Ramadana, akan samu cunkoson jama'ar da ke kaunar yin aikin ibada na Umrah a wata mai alfarma
- Saudiyya na ci gaba da kawo sauye-sauye a fannin da ya shafi ibada, musannan a cikin 'yan shekarun nan
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Kasar Saudiyya - M'aikatar Hajji da Umrah a kasar Saudiyya ta sanar da kimtse damar alhazai na yin Umrah sau biyu ko fiye da haka a cikin watan Ramadana.
Wannan doka an kawo ta ne don rage cunkoson jama'a a lokacin watan Ramadana, watan da aka fi ganin masu Umrah a kasar mai tsariki duk shekara, Saudi Gazette ta ruwaito.
Dalilin da yasa aka hana Umrah sau biyu a Ramadana
A cikin sanarwar da ma'aikatar ta fitar, ta bayyana dalilai dalla-dalla da suka kai ga kawo wannan sauyi baktatan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar:
“Ba za a ba maniyyata izinin yin Umrah sau biyu ko fiye da haka ba a cikin wata mai alfarma. Wannan yunkuri an yi shi ne don saukaka cunkoso da ba da dama ga sauran maniyyata don yin aikin Umrah cikin sauki da jin dadi a cikin wata mai alfarma."
A kafar da ake amfani da ita wajen cike fom din neman ziyarar Umrah, bincike ya nuna duk wanda ya yi ziyarar a cikin watan Ramadana bai samun damar sake cike fom din.
Ma'aikatar ta kuma bayyana fa'ida da muhimmancin yin Umrah a cikin watan Ramadana mai alfarma, rahoton Gulf News.
Babu hanyar yin Umrah sau biyu a Ramadana
Hakazalika, hukumar ta shawarci al'umma da su bi umarnin gwamnati don gujewa matsala tare da ba da hadin kai kowa ma ya samu damar yin Umrah a lokacin na Ramadana.
A bangare guda, babu wani tanadi da hukumar ta yi a manhajar Nusuk da ake cike fom din Umrah na sauya lokacin da aka kebe na yin ibadar.
Haka nan, manhajar bata da wani tanadin yin Umrah a wani lokaci na daban ba a cikin Ramadana ba, inda take katse damar yin rajista kai tsaye.
Batun hana nunawa duniya Tarawih daga Saudiyya
A baya, kungiyar malamai sun caccaki kasar Saudiyya kan yunkurin hana nunawa duniya sallar Tarawih da ake yi a Ramadana.
Wannan na zuwa ne tun bayan da Yariman Saudiyya ya sanar da cewa, za a rage yada karatun Al-Qurani da aka saba a kasar.
Saudiyya na fuskantar sauye-sauye ta fuskar addini, lamarin da ke ci gaba da daukar hankali a halin yanazu.
Asali: Legit.ng