Yadda Za a Bi a Maido Dalar Amurka N160 Daga N1600 Inji Masanin Tattalin Arziki
- Ahmed Adamu ya yi rubutu dauke da bayanin yadda za a iya magance tashin da kudin kasashen waje suka yi a Najeriya
- Malamin makarantar ya yi magana a inda ya fi wayau, ya ba CBN da gwamnati shawara a game da bangaren tattalin arziki
- Idan aka bi shawarar Dr. Adamu, yana ganin Dalar da ta tashi zuwa N1, 600 a yau za ta iya sunkuyawa zuwa kasa da N200
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Ahmed Adamu malami ne a jami’ar Nile da ke garin Abuja, ya kware a bangaren tattalin arziki, ya saba sharhi a fanninsa.
Kwanakin baya ya yi rubutu a shafinsa a game da yadda za a farfado da kimar Naira ganin Dala ta tashi daga N460 har zuwa N1, 600.
A matsayinsa na mataimakin Farfesa a jami’a, Dr. Ahmed Adamu ya koka kan yadda farashin kaya suke hauhawa alhali ana talauci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masanin tattali ya ce dole Naira ta mike
Masanin yake cewa darajar kudi ita ce kashin bayan tattalin arzikin duk wata kasa, kuma hakan yana da tasiri ga rayuwar ‘yan Najeriya.
Dr. Ahmed Adamu ya ce nauyin farfado da darajar Naira ya rataya ne a an wuyan duk wani ‘dan Najeriya, ba iyaka gwamnati kurum ba.
Duk da haka, yana ganin mafi yawan laifin yana kan Najeriya, ya ba da shawarar koyi da kasashen Jamus, Zimbabwe da Venezuela.
Yadda za a bi Naira ta karya Dala
Da farko masanin ya ce a maida hankali a kan noma da cigaban ma’adanai, ya ce bangarorin nan za su iya samar da daloli kamar mai.
"A dauki hayar filaye a ba ‘yan kasuwa daga kasashen ketare su noma amfanin da ake bukata a duniya, wannan zai zaburar da tattali."
"Gwamnatocin tarayya da na jihohi su ja ragamar samar da kayan amfanin da ke kawo kudi. Za mu iya samun kudin ketare a Najeriya."
- Dr. Ahmad Adamu
Bayan auduga, citta, ridi, masara, za a iya noma waken suya da sauransu. Alal misali kasar Thailand ta samu $9bn daga rogo a 2022.
Dr. Adamu ya kawo shawarar rage shigo da kayan ketare kamar yadda aka yi a baya, sai a fi bada karfi wajen dogara da kayayyakin gida.
Kwararren yana ganin babu laifi idan an daina amfani da kudin ketare wajen yin ciniki, za a iya yin cinikayya da kasashe da kayan gona.
Tinubu ya yi nadin mukamai a gwamnati
Labari ya zo cewa mutane biyu suka samu mukami daga Kano a jiya da Bola Tinubu ya tsige Sha’aban Sharada daga hukumar almajirai.
Nauyin kula da almajirai da marasa zuwa makarantun boko ya dawo hannun Janar Lawal Ja’afar Isa wanda ya taba yin gwamna a baya.
Asali: Legit.ng