'Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Jam'iyyar PDP, Bayanai Sun Fito
- Ƴan bindiga sun yi awon gaba da shugaban jam'iyyar PDP na jihar Edo, Tony Aziegbemi, a ranar Juma'a, 15 ga watan Maris 2024
- Tony ya faɗa tarkon ƴan bindigan ne jim kaɗan bayan ya kammala ganawa da gwamnan jihar, Godwin Obaseki
- Kwamishinan sadarwa na jihar ya tabbatar da sace shugaban jam'iyyar a cikin wata sanarwa, inda ya ce ana ƙoƙarin ganin an kuɓutar da shi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da shugaban jam’iyyar PDP reshen jihar Edo, Tony Aziegbemi.
An sace Aziegbemi ne ranar Juma’a jim kaɗan bayan wata ganawa da gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki a birnin Benin, babban birnin jihar, cewar rahoton gidan talabijin na Channels tv.
Gwamnatin Edo ta tabbatar da sace Tony
Duk da cewa har yanzu hukumomin ƴan sandan jihar ba su ce uffan ba kan lamarin, gwamnatin jihar Edo ta tabbatar da sace shugaban jam'iyyar a ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan sadarwa da wayar da kan jama'a na jihar Hon. Chris Nehikhare, ya fitar da wata sanarwa, inda ya ce gwamnatin jihar na ƙoƙarin ganin an sako shugaban jam'iyyar.
Ya ce gwamnati na aiki kafaɗa da kafaɗa da jami’an tsaro kan lamarin, inda ya bayyana sace Aziegbemi a matsayin wani abin takaici, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Gwamnati tana aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro domin ganin an sako shi lafiya tare da komawa ga iyalansa."
"Mun kuma ƙara sanya ido da kuma tsaurara matakan tsaro a fadin jihar domin tabbatar da cewa an daƙile waɗannan miyagun ayyuka tare da gurfanar da masu laifin a gaban kuliya.
Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?
Da aka tuntubi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Edo, Chidi Nwabuzor, ya ce nan ba da dadewa ba rundunar za ta fitar da sanarwa kan lamarin.
Sai dai ya kasa tabbatarwa ko karyata sace shugaban jam'iyyar.
Ƴan bindiga sun kai hari a Kaduna
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai sabon harin ta'addanci a jihar Kaduna.
Ƴan bindigan ɗauke da makamai sun farmaki ƙauyen Dogon-Noma na ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar, inda suka halaka mutane da dama.
Asali: Legit.ng