Kano: Kotun Shari'ar Musulunci Ta Raba Auren Sunnah Kan Dalili 1 Tak a Watan Ramadan

Kano: Kotun Shari'ar Musulunci Ta Raba Auren Sunnah Kan Dalili 1 Tak a Watan Ramadan

  • Kotun shari'ar Musulunci a jihar Kano ta raba auren Shamsiyya da Ghali bayan duk wani yunƙurin na yin sulhu ya ci tura
  • A zaman yanke hukunci a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, mai shari'a Malam Umar Lawal Abubakar, ya datse igiyoyin auren sabida mijin ya bar gida
  • Tun farko magidancin ya shaidawa Alkali cewa ya gudu ya bar gida ne saboda halin matsin da ake ciki kuma ya rasa motar da yake tuƙawa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Wata kotun shari'ar Musulunci a jihar Kano ta raba auren da aka ɗaura tsakanin wani direba, Zakari Ghali, da Shamsiyya Haruna kan dalilin rashin zama wuri ɗaya.

Kara karanta wannan

Iftaar: Abin da Shugaba Tinubu ya faɗawa gwamnoni a wurin buɗe bakin azumin Ramadan a Villa

Tun da farko Shamsiyya Haruna da ke zama a Unguwa Uku Quarters a jihar Kano ta shigar da ƙara gaban kotun Musulunci, inda ta roƙi alkali ya kashe aurenta.

Kotun musulunci ta raba aure a watan Ramadan.
Matsin tattalin arziki ya kashe aure a Kano Hoto: Shari'ar court
Asali: Getty Images

A rahoton jaridar Daily Trust, matar ta kuma roƙi kotun ta bar mata ƴaƴan da suka haifa su ci gaba da zama a hannunta bayan an raba aurenta da Malam Ghali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarta, tana neman rabuwa da kuma riƙe ƴaƴanta ne saboda mijinta, Ghali ya gudu ya bar ta da ƴaƴansu biyar babu abinda zasu ci.

Kotun musulunci ta raba ma'auratan

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun Musulunci, mai shari'a Malam Umar Lawal-Abubakar, ya ce kotu ra raba auren Shamsiyya da Ghali.

Alkalin ya kuma bayyana cewa kotu ta amince da raba auren ne bayan duk wani yunkuri da aka yi da taimakon iyayen mata da mijin bai cimma nasara.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kan ƙarar da aka shigar da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano

Tun da farko mai shari'a Lawal Abubakar ya umarci Ghali ya riƙa bai wa Shamsiyya Naira 90,000 don kula da yaransa duk wata, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Tsadar rayuwa ta sa miji ya tsere

Ghali ya shaidawa kotun cewa ya bar gida ne saboda matsin tattalin arziki da ake fama da shi a yanzu kuma ga tsadar rayuwa.

“Ba ni da kudin da zan ciyar da iyalina yanzu. Mai motar da nake safarar kaya na ɗan samu kudi ya ƙwace motarsa," in ji shi.

Kotu ta yanke hukunci kan naɗa kantomomi a Kano

A wani rahoton kuma kotu ta yanke hukunci kan ƙarar da aka nemi hana Abba Gida-Gida naɗa ciyamomin rikon kwarya a kananan hukumomin Kano.

Alkalin kotun mai shari'a Abdullahi Muhammad Liman, ya kori ƙarar a zaman ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262