APC Ta Gaji da Alkawarin Iska, Ta Shawarci Tinubu Kan Daukar Mataki Kan Shugabannin Tsaro
- Yayin da matsalar tsaro ke kara ta’azzara a Najeriya, kungiyar shugabannin jam’iyyar APC a kasar ta nuna damuwa kan matsalar
- Kungiyar ta shawarci Shugaba Tinubu kan hanyoyin da za a dakile matsalar cikin sauki tare da daukar mataki kan shugabannin tsaron
- Sakataren kungiyar, Alphonsus Eba shi ya bayyana haka yayin ganawa da Tinubu a yau Juma’a 15 ga watan Maris a fadar shugaban kasar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Kungiyar shugabannin jam’iyyar APC ta nuna damuwa kan yadda matsalar tsaro ke kara kamari.
Kungiyar ta shawarci Shugaba Tinubu da ya sallami dukkan shugabannin tsaron kasar da suka gaza wurin dakile matsalar.
Kungiyar ta koka kan matsalar tsaro
Shugabannin jam’iyyar sun bayyana haka ne a yau Juma’a 15 ga watan Maris a Abuja yayin ganawa da Shugaba Tinubu, cewar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakataren kungiyar, Alphonsus Eba ya bayyana cewa rashin tsaron ya yi kamari inda ya ce dole wasu su dauki laifin sakacinsu a matsalar.
“Maganar sace daliban makaranta a Kaduna, ya kara dagula matsalar tsaro da ya addabi kasar baki daya.”
- Eba Alphonsus
Shawarar da kungiyar ta ba Tinubu
“Wannan na daga cikin matsalolin da muka tattauna da Shugaba Tinubu, tabbas matsalar ta zama abin takaici a kasar.”
“Mun shawarci Tinubu cewa wannan lokaci ne da ya kamata ya dauki mataki kan shugabannin tsaro daban-daban domin dakile matsalar.”
- Alphonsus Eba
Eba ya ce sun ba Tinubu shawarar ce ganin cewa a matsayinsa na shugaban tsaron kasar, ba zai iya daukar bindiga domin yakar ‘yan bindiga ba, cewar Tribune.
Wannan ganawa na zuwa ne yayin da matsalar tsaro ke kara kamari duk wayewar gari a Najeriya wanda ke jawo rasa rayuka da dukiyoyi.
Kwastam ta kama muggan makamai a Legas
Kun ji cewa hukumar Kwastam ta yi nasarar cafke muggan makamai a tsibirin Tin-Can da ke jihar Legas.
Hukumar kuma ta cafke miyagun kwayoyi da kayan sojoji wanda aka yi kokarin shigo da su cikin Najeriya.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan bude iyakokin da ke tsakanin Najeriya da kasar Nijar ta sama da kan tudu.
Asali: Legit.ng