Iftaar: Abin da Shugaba Tinubu Ya Faɗawa Gwamnoni a Wurin Buɗe Bakin Azumin Ramadan a Villa

Iftaar: Abin da Shugaba Tinubu Ya Faɗawa Gwamnoni a Wurin Buɗe Bakin Azumin Ramadan a Villa

  • Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci gwamnoni su jingine siyasa kana su haɗa kai da gwamnatin tarayya domin gina ƙasar nan
  • Shugaban ƙasa ya bayyana haka ne a wurin buɗe baki 'Iftaar' na azumin Ramadan a fadarsa da ke Abuja ranar Alhamis
  • Gwamnonin sun yabawa gwamnatin Shugaba Tinubu bisa raba hatsi har tan 42,000 domin rage raɗaɗin tsadar rayuwar da ake fuskanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga gwamnoni su jingine saɓanin siyasa a gefe su hada kai da gwamnatin tarayya domin gina kasar nan.

Shugaba Tinubu ya yi wannan furucin ne a wurin shan ruwan azumi tare da gwamnoni wanda ya gudana a fadar shugaban ƙasa ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, 2024.

Kara karanta wannan

Tinubu ya canza tunani, ya janye sunan matar da ya naɗa a babban banki CBN, An gano dalili

Shugaba Tinubu tare da gwamnonin wasu jihohi.
Tinubu ya roƙi gwamnoni su haɗa kai da gwamnatin tarayya Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Babban mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin kafafen sada zumunta na zamani, D. Olusegun ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya wallafa a manhajar X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya ja hankalin gwamnoni a Villa

Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin ajiye batun siyasa tare da tunkarar harkokin mulki, inda ya bayyana bukatar hadin kai da aiki tare a tsakanin masu ruwa da tsaki.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Ajuri Ngelale, kakakin shugaban ƙasa ta hakaito Tinubu na cewa:

"Tun da mun fahimci akwai bukatar mu haɗa karfi da ƙarfe wajen gina ƙasar mu, ya kamata mu sani cewa lokacin siyasa ya wuce, yanzu magana ce ta shugabanci.
“Mu ‘yan uwa daya ne kuma ƴan gida ɗaya, muna zaune a gida daya, amma muna kwana a ɗakuna daban-daban. Dole ne mu hada kai sannan mu nuna wa juna soyayya."

Kara karanta wannan

Abin sha'awa: Bola Tinubu ya yi buɗa baki 'Iftar' na azumin Ramadan tare da wasu gwamnoni a Villa

Da yake jan hankali kan muhimmancin watan Ramadan da lokacin azumi ga Kiristoci, Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya su yi amfani da wannan dama wajen tuba, addu’o’i, da kuma bayar da sadaƙa ga mabuƙata.

Gwamnoni sun ɗauki alƙawari

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya yabawa gwamnatin tarayya kan rabon hatsi tan 42,000.

Ya kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi domin tunkarar kalubalen da ya addabi al'umma.

Dangane da batun tallafin albashi ga ma'aikata, shugaban NGF ya yi alƙawarin cewa gwamnoni za su yi abinda ya dace.

Tinubu ya fasa naɗa Onwudiwe a CBN

A wani rahoton na daban Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya janye naɗin Ruby Onwudiwe a matsayin mambar majalisar gudanarwa ta babban bankin Najeriya (CBN).

Rahotanni sun nuna cewa shugaban ƙasa ya ɗauƙi wannan matakin ne biyo bayan matsin lambar da yake fuskanta daga mambobin jam'iyyar APC mai mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262